Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jama’a kan wata sanarwa ta bogi da ake yaɗawa a kafafen sadarwa, wadda aka danganta da hukumar kan batutuwan da suka shafi jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohi shida.
Jihohin da abin ya shafa su ne Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da Kano.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa sanarwar da ake yaɗawa ba gaskiya ba ce, kuma ba ita ta fitar da ita ba.
Saboda haka, INEC ta buƙaci jama’a da su yi watsi da sanarwar tare da guje wa sake yaɗa ta.
Hukumar ta shawarci jama’a da su riƙa samun sahihan bayanai daga sanarwar manema labarai da sauran bayanan da take fitarwa ta kafafen sadarwarta na hukuma.
Kafafen sun haɗa da shafinta na intanet, www.inecnigeria.org; shafinta na Facebook mai suna INEC Nigeria; da shafukanta na X da Instagram, waɗanda ke amfani da sunan @inecnigeria.
Haka kuma, jama’a za su iya samun sahihan bayanai ta tashar labarai ta hukumar mai adireshin www.inecnews.com.
INEC ta ƙara jaddada cewa duk wani bayani da ke nuna cewa ta fitar da sanarwa ta musamman kan ’yan takarar gwamna a jihohin da aka ambata ƙarya ne.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da tabbatar da sahihancin bayanan da suka shafi zaɓe ta hanyar amfani da kafafenta na hukuma, domin guje wa ruɗuwa da bayanan ƙarya.
Ta kuma bayyana cewa masu buƙatar ƙarin bayani za su iya tuntuɓarta ta cibiyar kiran waya mai lamba 0700-CALL-INEC (0700-2255-4632), ko kuma ta aika saƙo zuwa lambar 4632.
Sauran lambobin wayar da hukumar ta bayar su ne 090844444333 da 09050858629, yayin da adireshin imel ɗinta shi ne [email protected].
INEC ta sake jaddada aniyarta ta samar wa jama’a sahihan bayanai, tare da kira gare su da su yi watsi da sanarwar ta bogi, su kuma riƙa dogaro da bayanan da aka fitar ta kafafenta na hukumar kawai.













