Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su zaɓi jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027 idan ba za ta iya cika alƙawarin da ta ɗauka ba.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) na shekarar 2026 da aka gudanar a Fatakwal, Jihar Ribas.
Ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su zaɓi shugabanni bisa cancanta da irin ayyukan da suka gudanar a baya ba.
Ya kuma buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su guji zaɓar ‘yan takara saboda ƙabila, yanki ko asalin inda suka fito.
A cewarsa, ya kamata a tantance shugabannin siyasa bisa abubuwan da suka cimma yayin da suke kan mulki.
Amaechi ya ce zai yi wuya jam’iyyun adawa su yi haɗaka guda saboda ‘yan siyasa da dama na da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa kuma ba sa son janye wa wasu.
Tsohon gwamnan na Jihar Ribas, ya kuma kare tarihinsa a harkar mulki, yana cewa har yanzu ana iya ganin ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta gudanar a jihar.














