A cikin shekara 9 da suka wuce a tsakanin 2015 zuwa 2024, Nijeriya ta yi asarar ‘yan majalisar tarayya akalla 29, wadand suka mutu a kan kujerunsu.
Sanatoci 8 da ‘yan majalisar wakilai 21 sun mutu tun lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta amshi gwamnati.
- Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Karshen Matsin Rayuwa – Gwamnan Bauchi
- Za Mu Raba Wa Talakawa Kyautar Kudi – Gwamnatin Tarayya
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa marigayan ‘yan majalisau da suka fito daga sassan daban-daban na kasar nan, galibinsu sun mutu ne sakamakon rashin lafiya, yayin da daya ya mutu sakamakon harbin bindiga.
Yayin da wasu suka mutu a nan gida Nijeriya, inda wasu kuma suka mutu a kasashen ketare.
Sanata Ahmed Zanna (1955-2015)
Zanna, Sanata ne mai wakiltar Borno ta tsakiya, ya rasu a shekarar 2015.
Kafin rasuwarsa, Zanna ya yi fama da rashin lafiya da ba a bayyana cutar da ke damunsa ba. Ya rasu ne bayan ya dawo daga kasar Amurka inda ya je neman magani.
Sanata Isiaka Adetunji Adeleke (15 Janairun 1955 – 23 Afrilun 2017)
Adeleke ya kasance sanata har sau biyu kafin rasuwarsa. Ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP a mazabar Osun ta yamma, daga 2007 zuwa 2011, sannan an sake zabensa a karkashin tutar jam’iyyar APC a 2015.
Dan majalisan ya samu bugun zuciya kafin ya mutu a ranar 23 ga Afrilu, 2017 a asibitin Biket da ke Osogbo Jihar Osun.
Sanata Ali Wakili (1960 -2018)
Wakili wanda ya yi ritaya daga hukumar kwastam, ya wakiltar Bauchi ta kudu a majalisa ta 8, inda ya rasu a ranar 17 ga Maris, 2018.
Sanata Benjamin Uwajumogu (30 ga Yunin 1968 – 18 ga Disambar 2019)
Uwajumogu ya rasu ne sakamakon rashin lafiya. Ya kasance mai wakiltar mazabar Imo ta arewa a majalisar dattawa ta 9 kafin rasuwarsa
Sanata Ignatius Datong Longjan (19 Mayu 1944 – 10 Fabrairu 2020)
Longjan ya kasance jami’in diflomasiyya wanda ya zama sanata, ya samu shiga majalisar dattawa a shekarar 2019. Yana wakiltar mazabar Filato ta kudu har zuwa rasuwarsa a shekarar 2020.
Ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan Jihar Filato daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Sanata Rose Okoji Oko (27 Satumba 1956 – 23 Maris 2020)
Oko ta rasu ne a ranar 23 ga Maris, 2020 yayin da yake wakiltar Kuros Ribas ta arewa.
Ta kasance ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yala/Ogoja a majalisar tarayya ta 7 a Nijeriya.
An zabe ta a matsayin wakiliya mace ta farko daga mazabarta a watan Yunin 2011, kuma ta rike mukamin mataimakiyar shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi.
Sanata Adebayo Sikiru Osinowo (28 Nuwamba 1955 – 15 Yuni 2020)
Har zuwa rasuwarsa, Osinowo ya wakilci gundumar Legas ta gabas. Osinowo ya kasance dan kasuwa ne kuma a baya ya taba zama dan majalisar dokokin Jihar Legas.
Sanata Patrick Ifeanyi Ubah (3 ga Satumba, 1971 – Yuli 27, 2024)
Ubah, ya kasance hamshakin dan kasuwa, ya rasu a kasar Ingila a ranar 27 ga Yuli, 2024. Ubah dai ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki daga jam’iyyar YPP a bara. An dai sake zabensa a majalisar dattawa ta 10 karkashin jam’iyyar YPP. An dai cire sunan marigayin ne lokacin da yake neman tikitin takarar gwamnan Jihar Anambra a jam’iyyar APC.
A zauren majalisar wakilai kuwa;
Hon Olatoye Temitope Sugar (1973-2019)
Olatoye ya wakiltar mazabar tarayya ta Lagelu / Akinyele kafin rasuwarsa. Ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin majalisar kan ci gaban birane da tsare-tsare na yanki. An harbe marigayin ne a unguwar Lalupon da ke wajen garin Ibadan a karamar hukumar Lagelu ta Jihar Oyo, a ranar 9 ga watan Maris, 2019. An garzaya da shi asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan, inda daga bisani ya mutu sakamakon raunukan harbin bindida.
Hon Jafa’aru Iliyasu
Iliyasu ya wakiltar mazabar Magama/Rijau ta Jihar Neja kafin rasuwarsa a watan Disambar 2019.
Har ya zuwa rasuwarsa, Jafa’aru ya kasance dan jam’iyyar APC mai mulki, wanda rahotanni suka ce ya mutu ne lokacin da yake barci bayan ya dawo Abuja.
Hon Mohammed Adamu Fagen Gawo (1950- 2019)
Gawo ya rasu ne a lokacin da yake wakiltar mazabar Garki/Bubara ta Jihar Jigawa a karo na biyu. Ya rasu ne kasa da wata guda da rasuwar dan majalisa Ja’afaru Iliyasu.
Rahotanni sun bayyana cewa, ya rasu ne a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a lokacin da ya tafiya neman magani.
Hon Bello Sani (1966- 2017)
Bello ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi ta Jihar Katsina kafin rasursa a ranar 15 ga watan Fabrairun 2017, wanda ya mutu yana da shekaru 51. An bayyana cewa dan majalisar ya yi fama da rashin lafiya na tsawon watanni kafin ya rasu. Dan majalisar ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke Kano.
Haka kuma, ya sha fama da ‘yan bindiga, inda aka yi garkuwa da shi kafin mutuwarsa a lokacin da yake tuka mota zuwa gonarsa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, wanda daga baya aka sake shi.
Hon Umar Buba Jibril (1961- 2018)
Jibril ya wakilci mazabar Lokoja/Kogi/Koton Karfe, ya kasance mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar. Ya rasu yana da shekaru 57 a duniya a wani asibitin Abuja bayan ya sha fama da jinya.
Hon Elijah Adewale (1951-2018)
Kafin rasuwarsa, Adewale ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Ifako Ijaiye a Jihar Legas. Rahotanni sun bayyana cewa ya kwanta dama ne a safiyar ranar 21 ga watan Yulin 2016 a gidansa da ke Abuja. An bayyana cewa ya halarci taron majalisar wakilai da yammacin ranar da ta gabata kafin rasuwarsa.
Hon Musa Baba-Onwama
Marigayi dan majalisar ya wakilci mazabar Nasarawa/Toto ta Jihar Nasarawa kafin rasuwarsa. Ya rasu yana da shekaru 50 a duniya.
Hon Abdullahi Wammako (1968- 2017)
Wammako, wanda ya zama dan majalisa a karon farko, ya wakilci mazabar tarayya ta Kware/Wammako kafin mutuwarsa.
Ya tsaya takara kuma ya lashe zabe a 2015 na ‘yan majalisa a karkashin jam’iyyar APC. Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Hon Yuguda Hassan-Kila (1951-2021)
Hassan-Kila ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram ta Jihar Jigawa daga shekarar 2015 zuwa 2021, ya kasance shugaban kwamitin kwastam na majalisar dokoki. Ya mutu ne bayan rashin lafiya da ba a bayyana ba a watan Satumba, 2021, yana da shekaru 70.
Hon Prestige Ossy (1965-2021)
Har zuwa rasuwarsa, Ossy ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Aba ta Arewa/Kudu na Jihar Abiya. An ruwaito cewa yam utu ne a ranar 7 ga Fabrairun 2021 a ksar Jamus, inda ya jinya a kasar.
Hon Adedayo Omolafe (1964-2021)
Omolafe, wanda ke wakiltar mazabar Akure ta Kudu/Akure ta Arewa a Ondo a majalisar wakilai, ya rasu ne a lokacin hutun shekara ta 2021.
Hon Haruna Maitala (1954-2021)
Hon. Maitala, wanda ke wakiltar mazabar Jos ta Arewa/Bassa ta Jihar Filato, ya rasu ne a ranar 2 ga Afrilu, 2021 a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Abuja zuwa Jos.
Hon Suleiman Lere
Lere, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Lere ta Kaduna, ya rasu ne bayan gajeruwar jinya a ranar 6 ga Afrilu, 2021. Yana da shekaru 53.
Hon Ekpenyong Bassey
Bassey, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Oron ta Jihar Akwa Ibom, ya rasu ne a ranar 24 ga Afrilu, 2022.
Hon Abdulkadir Danbuga
A ranar 11 ga Oktoba, 2023, Danbuga, wanda ke wakiltar mazabar Isa/Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. Yana da shekaru 63.
Hon Isa Dogonyaro
Dogonyaro, wanda ke wakiltar mazabar Garki/Babura a Jihar Jigawa, ya rasu ne a ranar 10 ga Mayu, 2024, yana da shekaru 46 a Abuja bayan rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Har zuwa rasuwarsa, Dogonyaro ya kasance mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan yaki da cutar kanjamau, tarin fuka da kuma yaki da zazzabin cizon sauro.
Musiliudeen Akinremi (1973-2024)
A watan Yuli, Akinremi, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ibadan ta arewa a Jihar Oyo, ya rasu a Abuja.