Rundunar ‘Yansandan Jihar Zamfara ta ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 a wani samamen haɗin gwiwa a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara.
‘Yansanda sun ce jami’an rundunar ta musamman, da jami’an Community Protection Guard da Civilian JTF ne suka gudanar da aikin.
Jami’an tsaron sun tare wasu ‘yan bindiga da ke kan babura biyar tare da mutanen da suka yi garkuwa da su a kusa da ƙauyen Tashar Lawali.
An yi musayar wuta bayan ‘yan bindigar sun fara buɗe wa jami’an tsaron wuta.
Rundunar ta ce an kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da kuma gidan alburusanta.
An ceto mutanen biyu ba tare da sun ji rauni ba, yayin da sauran ‘yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji.
Babu wani jami’in tsaro da ya ji rauni.
Rundunar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama ‘yan bindigar da suka tsere.














