ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yanayin Bunkasar Hada-hadar Cinikayyar Sin Ya Shaida Karkon Manufofin Raya Tattalin Arzikin Kasar

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Sin

Yayin da duniya ke fuskantar yanayi na rashin tabbas, da manyan sauye-sauye a yanayin cudanyar cinikayya tsakanin kasa da kasa, wadanda ke haifar da koma baya, da tafiyar hawainiya a wasu sassa na kasuwancin duniya, a daya hannun harkokin tattalin arziki a kasar Sin na bunkasa yadda ya kamata.

Wasu alkaluman baya bayan nan da mahukuntan kasar Sin suka fitar, sun nuna yadda a watan Mayu da ya gabata, hada-hadar fitar da hajoji zuwa kasashen waje daga Sin ta karu da kaso 19.4 bisa dari kan na shekarar da ta gabata, kuma adadin ya dara kaso 14.1 da aka samu a watan Afirilun bana. Wani abun da manazarta suka bayyana mamakinsa ma shi ne yadda addadin hada-hadar shigo da hajoji cikin kasar ya dara na fitar da su, inda alkaluman suka nuna karuwar shigo da hajojin zuwa kaso 27.4 bisa dari a watan Mayu, sama da kaso 25.3 da aka samu a watan Afirilu.

Bugu da kari, fadadar harkokin cinikayyar kasar ya kai kaso 16.9 bisa dari, inda darajarsa a duk wata cikin watsanni uku a jere, ke kaiwa sama da kudin Sin yuan tiriliyan hudu, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 587. Kuma da wannan sakamako, karuwar jimillar ci gaban cinikayyar kasar Sin cikin watanni biyar na farkon shekarar bana ya kai kaso 15.3 bisa dari.Irin wannan ci gaba ya saba da tunanin wasu sassan yammacin duniya dake kallon kasar Sin a matsayin mai dogaro kacokan kan fitar da hajoji fiye da kima zuwa kasashen ketare.

ADVERTISEMENT

Maimakon haka, alkaluman sun shaida yadda ci gaban fannin cinikayya, da hada-hadar raya tattalin arzikin kasar Sin ke tafiya bisa daidaito, da inganci da kuma goyayya mai tsafta.Ko shakka babu, wannan ba batu ne dake nuna karuwar adadin hajoji da Sin ke fitarwa ba ne kadai, maimakon haka batu ne dake shaida irin ci gaba da kasar ke samu ta fuskar shige da ficen kayayyaki, da hidimomi da duniya ke bukata, a yayin da akasarin manyan kasashe masu wadata ke fadi-tashin cimma irin wannan sakamako.

Har ila yau, nasarorin da Sin din ta cimma a fannin shige da ficen hajoji, tare da kasashe musamman masu tasowa, na nuni ga nasarar cudanyar abokan cinikayya masu cimma moriyar juna.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Don haka, fatanmu a nan shi ne kamar yadda kasar Sin ke kara aiwatar da managartan manufofin bunkasa alakar cinikayya, sauran manyan kasashe masu arziki ma za su rungumi tsarin cudanya mai karko, mai kunshe da kirkire-kirkire da game dukkanin sassan kasa da kasa. Irin wanda zai rika haifar da moriyar bai daya da bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Japan Ta Kwaye Lullubin Da Take Fakewa Da Shi Wajen Kiran Kanta Mai Kaunar Zaman Lafiya

Japan Ta Kwaye Lullubin Da Take Fakewa Da Shi Wajen Kiran Kanta Mai Kaunar Zaman Lafiya

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.