Yanayin iska da ruwa a kasar Sin ya ci gaba da ingantuwa a watanni bakwai na farko na shekarar 2026, yayin da kasar ta kara kaimi wajen rage gurbacewar iska da kuma kare albarkatun ruwa, kamar yadda ma’aikatar kiyaye muhalli da tsarin rayuwar halittu ta bayyana a yau Alhamis.
Huang Runqiu, ministan kiyaye muhalli da tsarin rayuwar halittu na kasar Sin, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, matsakaicin mizanin barbashin da ake samu a iska na PM2.5 wanda muhimmin ma’auni ne na auna gurbacewar iska, ya ragu da sikilen mikrogram 1.8 a kowace kyubik mita, cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a shekarar da ta gabata; inda hakan ke nuna an samu raguwarsa da kashi 6.2 cikin dari.
Har ila yau, ma’aikatar ta bayyana cewa a tsakanin wannan lokaci, an sanya kashi 86.5 na wuraren da ake sa ido a kan ruwan da ke saman kasa a cikin matakai masu daraja ta I zuwa ta III, wanda hakan ke nuna inganci mai kyau da aka samu karuwarsa da kashi 2.4 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














