ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Suke Kara Ingiza Hada-Hadar Cinikayya Tsakanin Sin Da Nahiyar Afirka

by CGTN Hausa
4 weeks ago
Sin

Tun daga karuwar hada-hadar albarkatun gona masu inganci da ake shigarwa kasar Sin daga sassan nahiyar Afirka, da cinikayyar na’urorin samar da makamashi kirar Sin dake kara samun kasuwa a sassan Afirka, zuwa harkokin gine-ginen zamani na Sin masu taimakawa ci gaban ababen more rayuwa a kasashen Afirka, muna iya fahimtar ci gaban da hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da Afirka ke kara haifarwa ga bangarorin biyu.

A shekarun baya bayan nan, tsarin cinikayya tsakanin Sin da nahiyar Afirka na kara kyautata. Wasu alkaluma da hukumar kwastam ta Sin ta fitar sun tabbatar da cewa, a cikin watanni 6 na farkon shekarar bana, darajar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta kai kudin Sin tiriliyan 1.41 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 208, wanda ya kafa matsayin tarihi.

Wannan muhimmin mataki na tarihi na da matukar kima, ba kawai ta fuskar adadin kudaden cinikayya ba, har ma da muhimmin fannin sauyin tsarin cinikayyar sassan biyu. Musamman duba da yadda kasashen Afirka ke kara samun zarafi na fitar da tarin hajojinsu zuwa kasar Sin, wanda hakan ke nuni ga inganci, da kuma yalwar hajojin da nahiyar ke samarwa, yayin da karuwar shigar da hajojin Sin cikin nahiyar, wadanda suka hada da na fasahohi, da na ayyukan masana’antu ke shaida karin karbuwar hajojin Sin masu tallafawa ci gaban Afirka a tsakanin al’ummun nahiyar. Tabbas, sakamakon wannnan ci gaba a bayyane yake, wato hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ya ginu ne kan tsari na cude-ni-in-cude-ka, yayin da kasuwannin sassan biyu ke kara dinkewa da dunkulewa waje guda.

ADVERTISEMENT

A gabar da ake cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka a bana, Sin ta kaddamar da manufar soke harajin fito kan hajojin kasashen Afirka 53 da ke da huldar diflomasiyya da ita. Wanda hakan ya sanya Sin din zama babbar kasa a duniya ta farko da ta aiwatar da irin wannan manufa mai matukar alfanu ga al’ummun Afirka.

Yayin da tsarin cinikayyar kasa da kasa ke sauya salo, kuma wasu sassa ke daukar matakai na kariyar cinikayya, Sin na ci gaba da fadada bude kofofinta ga nahiyar Afirka. Kuma wadannan matakai sun samar da karin dama ta daidaituwar yanayin kasuwa, da karin damarmakin fadada hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Sin
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Next Post
Kasashe 16 Na Duniya Za Su Halarci Gasar Wasannin Motsa Jiki Na Mutum-Mutumin Inji Masu Siffar Dan Adam Karo Na Biyu

Kasashe 16 Na Duniya Za Su Halarci Gasar Wasannin Motsa Jiki Na Mutum-Mutumin Inji Masu Siffar Dan Adam Karo Na Biyu

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.