Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutane shida da ake zargi bayan wani rikici tsakanin wasu ‘yan daba daga bisani suka kai hari kasuwar wayoyin hannu ta ‘Farm Centre’ da ke Kano.
A jiya Litinin, mun rahoto muku yadda wasu ‘yan daba ɗauke da muggan makamai suka kai hari kasuwar da rana tsaka, inda suka kwashe kayayyaki masu daraja mallakin ‘yan kasuwa, kwastomomi da masu wucewa.
Rahotanni sun nuna cewa waɗannan ‘yan daban sun halarci wani taron siyasa ne da aka gudanar kusa da kasuwar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Talata, rundunar ta ce ta kama shida daga cikin waɗanda ake zargin tare da daƙile harin.
Kiyawa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan samun kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun taru domin yin faɗa a yankin Gyadi-gyadi, wata unguwa da ke kusa da kasuwar, kafin daga bisani su afkawa ‘yan kasuwar.














