Za a gudanar da taron tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka karo na 7 a babbar cibiyar taro ta Beijing daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Agusta. Kwararru da wakilan manyan kamfanonin fasaha za su hallara a wurin taron, domin musayar bayanai kan sabbin nasarorin da aka samu a fannin kirkire-kirkiren fasahar AI da kuma yadda ake amfani da ita a zahiri.
Ta hanyar gabatar da shirye-shirye, da daidaita sakamakon da suka dace da juna, da kuma tattaunawa kan hadin gwiwa, dandalin zai kafa wani ingantaccen dandamali domin musayar fasahar hada sauti da bidiyo ta Sin da Afirka, da kulla alakar masana’antu, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
Manufar hakan ita ce nuna cikakken karfin sabbin fasahohin zamani na kaasar Sin a fannin fasahar hotuna da bidiyo masu matukar inganci (UHD), da samar da shirye-shirye da abubuwan da za a yada bisa fasahar AI (AIGC), da kuma watsa shirye-shirye da gudanar da ayyukan hada su ta hanyar amfani da fasaha, ta yadda za a kara sabon kuzari ga karfafa cinikayyar ayyukan rediyo da talabijin na hada sauti da bidiyo ta Sin da Afirka, da kuma habaka hadin gwiwar masana’antu a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














