ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zama Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki!

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago

Tun kafin barkewar tashin hankali na baya bayan nan a gabas ta tsakiya, masharhanta suke ta bayyana damuwa game da yiwuwar fuskantar mummunan yanayi idan har ba a kai zuciya nesa ba.

Masana da dama sun yi hasashen bazuwar tasirin yakin a dukkanin sassan gabas ta tsakiya, muddin Amurka ta kaddamar da hare-hare kan Iran.

To sai dai ana tsaka da tattaunawa, sai kwatsam Amurka da Isra’ila suka fara kaddamar da hare-hare kan kasar ta Iran, nan take kuma Iran din ta fara mayar da martani kan kawayen Amurka dake samar mata da sansanonin kaiwa Iran din hare-hare dake yankin baki daya.

ADVERTISEMENT

Wannan lamari ya kasance mafari na dauki ba dadi da aka kwashe sama da kwanaki 40 ana yi, kafin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta makwanni biyu, aka kuma fara tattaunawar da ba ta kai ga haifar da sakamakon da ake fata ba.

Tattaunawar da aka gudanar tsakanin wakilan Amurka da na Iran a ranar 14 ga watan nan a kasar Pakistan, ta zamo irinta ta farko tun bayan barkewar rikicin, kuma a yanzu haka, gabanin sake tattaunawa a karo na biyu, Amurka ta yi ikirarin toshe tashohin jiragen ruwa dake Iran a dukkan fannoni, a wani mataki da sassan kasa da kasa ke ganin zai kara tsananta halin da ake ciki.

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu

Yayin da ake fatan ganin sassan biyu sun sake gudanar da tattaunawa ta kai tsaye kuma cikin nasara, wani abun lura shi ne yadda wannan danbarwa ta haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya, ba wai kawai kasashen dake shiyyar ta gabas ta tsakiya ba.

Mun dai ga yadda wannan tashin hankali ya gurgunta tsarin gudanar hada-hadar cinikayya na duniya, ciki har da na kasashen yammacin duniya masu karfin ci gaba.

Rufe mashigin Hormuz, ya illata hada-hadar albarkatun makamashi na duniya, wanda hakan ya haifar da hauhawar farashin albarkatun mai a kasuwannin duniya, da tsadar kayayyaki a kusan dukkanin kasashe, ciki har da masu tasowa wadanda da dama can ke cikin yanayi na matsi.

Hakan kuma na da nasaba da yadda makamashi ke da alakar kai tsaye da harkokin sufuri, da sarrafa hajojin masana’antu, da rarraba hajojin zuwa sassan kasa da kasa, da noma, da sayayyar ababen bukatun al’umma na yau da kullum.

Wani muhimmin darasi game da wannan tashin hankali, da ya kai ga rufe mashigin Hormuz, shi ne rashin kwanciyar hankali a wani bangare na duniya, na iya haifar da mummunan tasiri ga duniya baki daya.

Wato dai wannan yaki na gabas ta tsakiya ya zamewa duniya darasi game da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, da walwala a dukkanin sassan kasa da kasa.

Kamar dai yadda Bahaushe kan ce “Zama Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki!”Wannan danbarwa ta zamewa duniya babban kalubale, ta yadda tasirin tashin hankalin na gabas ta tsakiya bai takaita ga yankin kadai ba, maimakon hakan ya haifar da matsalar tattalin arziki da mai yiwuwa a jima ana dandana illar ta. (Saminu Alhassan)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu
  • Sulaiman
    Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Kammala Taro Na 13 Na Dandalin Tattauna Tsaro Na Xiangshan A Beijing
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Na 23
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

MASU ALAKA

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya
Daga Birnin Sin

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

September 17, 2026
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu

September 17, 2026
Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa

September 17, 2026
Next Post
Tanzania Na Shirin Jan Hankalin Adadi Mai Yawa Na Sinawa Masu Yawon Bude Ido

Tanzania Na Shirin Jan Hankalin Adadi Mai Yawa Na Sinawa Masu Yawon Bude Ido

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

September 18, 2026
Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

September 18, 2026
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 18, 2026
Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

September 18, 2026
ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

September 18, 2026
Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

September 18, 2026
Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

September 18, 2026
Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

September 18, 2026
Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

September 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.