Babban dan majalisar dokokin kasar Sin Zhao Leji, ya gana da shugaban kasar Botswana Duma Gideon Boko, kana ya zanta da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé jiya Talata a nan birnin Beijing.
Yayin da yake zantawa da mista Boko, Zhao, wanda shi ne shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jamaar kasar Sin NPC, ya ce Botswana muhimmiyar kawar kasar Sin ce a kudancin nahiyar Afirka, kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da Botswana wajen tabbatar da nasarar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Kazalika, Zhao ya ce majalisar NPC a shirye take wajen karfafa hadin gwiwa tare da majalisar dokokin Botswana, da musayar kwarewar da aka samu game da ci gaban dimokaradiyya da dokoki, da samar da tsare-tsaren kare doka don tabbatar da hadin gwiwar sassan biyu.
Yayin da yake zantawa da mista Faure kuwa, Zhao cewa ya yi Sin a shirye take ta yi aiki tare da Togo, karkashin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da zurfafa amincin siyasa, da fadada hadin gwiwar cimma moriyar juna, da yaukaka musayar kut-da-kut tsakanin alummunsu.
Zhao, ya kara da cewa majalisar NPC, a shirye take ta karfafa musaya, da koyi da juna tare da majalisun dokoki biyu na kasar Togo, da karfafa hadin gwiwa karkashin tsarin cudanyar mabanbantan sassa, ciki har da hadakar ayyuka na majalisu daban daban. (Saminu Alhassan)













