A nasa jawabin yayin ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa yana ganin alamun nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, tare da bayyana shirinsa na jagorantar yunƙurin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.
Adeleke, wanda a baya-bayan nan ya koma tare da APC, ya ce babu wanda zai iya dakatar da wannan yunƙuri, yana mai alƙawarin cewa magoya bayan Tinubu za su yi murnar komawa fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock.
Gwamnan, wanda aka san shi da rawa a wajen tarukan jama’a, ya ce za a gudanar da yaƙin neman zaɓen cikin waƙoƙi da raye-raye.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su ƙara ba shugaban ƙasa lokaci domin manufofin sauye-sauyen da yake aiwatarwa su fara haifar da sakamako, yana mai amincewa cewa aiwatar da manufofin bai kasance cikin sauƙi ba.
Adeleke ya ce ya shiga wannan yunƙuri ne saboda yana son a ɗauki matakai na zahiri maimakon yawan magana, yana mai cewa tuni ya fara aikinsa a wannan fanni.














