Galibin kasashe suna fara alaka da juna ne sakamakon yarjejeniyar diflomasiyya, amma duk da cewa diflomasiyya a tsakanin Sin da Masar an kafa ta ce a hukumance yau shekaru 70 da suka gabata, alakar al’ummomin kasashen biyu ta girmi hakan nesa ba kusa ba, idan aka yi la’akari da cewa Sin da Masar wayewar kai ce guda biyu da suka ba da gagarumar gudunmawa ga tarihin bil’adama a doron kasa.
Akwai kamanceceniya a tsakanin wayewar kan kasashen biyu idan aka dubi yadda Kogin Nilu ya kasance tushen wayewar kai ta Masar, yayin da kogunan Yangtze da Rawaye su kuma suka taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar wayewar kan kasar Sin. Kazalika, idan aka waiwayi kasuwancin hanyar siliki da gano kayayyakin kasar Sin a Fustat, za a kara tabbatar da cewa mu’amalar al’ummomin biyu tana da dogon tarihi.
Saboda haka, lokacin da Masar ta zama kasa ta farko a yankin Larabawa da Afirka da ta kulla huldar diflomasiyya da Jamhuriyar Jama’ar Sin a ranar 30 ga watan Mayun 1956, ba wai an fara wata alaka daga tushe ba ce, abin da aka yi shi ne mayar da wata tsohuwar fahimtar juna tsakanin wayewar kai biyu zuwa dangantakar diflomasiyya ta zamani.
Kazalika, yana da matukar ban sha’awa yadda aka ci gaba da yaukaka wannan zumunci har zuwa yau da Shugaba Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Masar bisa gayyatar shugaban kasar Abdel Fattah El-Sisi, wanda a cikin rubutaccen jawabin da Xi ya bayar, ya tabo batun yadda kasashen biyu suke mara baya ga juna a harkokin kasa da kasa.
Idan ba a manta ba, a lokacin rikicin mashigin Suez na shekarar 1956, Sin ta nuna goyon baya ga matsayin Masar, kuma sannu a hankali dangantakar da ta fara da fahimtar juna ta siyasa ta koma hadin gwiwar tattalin arziki, inda a yau kamfanonin Sin ke taka rawa wajen bunkasa yankin tattalin arziki na Suez.
Hadin gwiwar kasashen biyu ya kai ga fannoni da dama, ciki har da sufuri, fasaha, ilimi, al’adu, raya birane da fasahar sararin samaniya wadanda suka kasance daga cikin misalan da ke nuna cewa dangantakar tana kara samun tagomashi.
Cika shekaru 70 na diflomasiyyar Sin da Masar ya zarce batun amincewar siyasa saboda dadadden zumuntar al’ummunsu, kuma wata dama ce ta sake tambayar abin da wasu manyan wayewar kai biyu masu dadadden tarihi za su iya ginawa cikin hadin gwiwa a karni na 21.
Bugu da kari, abin da ya fara a matsayin cudanyar wayewar kai tun zamanin da, sannan ya koma huldar diflomasiyya a 1956, a halin yanzu yana da damar zama wata muhimmiyar gada mai muhimmanci tsakanin Sin da Masar, har ma da dukkannin kasashen Afirka.
Kuma watakila babban darasin cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyyar shi ne: zumunci mai dorewa da ake ci gaba da gina kyakkyawar makomar bil’adama ta bai-daya a kansa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














