ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar PNGI Ta Yaba Wa Bayo Ojulari Bisa Nasarorin Gyare-gyare Da Aka Fara Samu A NNPC

by Bello Hamza and Sulaiman
8 months ago
NNPC

Ƙungiyar ci gaban ƙarni mai zuwa ta ‘Progressive Next Generation Initiative (PNGI)’ ta jinjina wa shugaban rukunin kamfanin man fetur na ƙasa NNPC, Bashir Bayo Ojulari bisa abin da suka kira da dogon tunanin sa wajen ƙaddamar da shirye-shiryen da za su inganta babban kamfanin mai na ƙasa, tun bayan kama aikin sa a ranar 2 ga watan Afrilun 2025.

A cikin wata sanarwa ta manema labarai da aka fitar a Litinin ɗin nan, 26 ga watan Janairu, 2026 mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Hon. Jeffery Omoh Ozemegwa, ƙungiyar ta bayyana cewa shugabancin Ojulari na ɗan ƙanƙanin lokaci, ya samar da ƙyaƙƙyawar fata a harkar mai da gas, yayin da ya ke shimfiɗa turbar ci gaba, aiki da gaskiya da kuma samar da hanyoyin ci gaban ƙasa.

Ƙungiyar PNGI ta kuma bayyana jagoran kamfanin na NNPC a matsayin mutum mai kishin ƙasa, hangen nesa, sannan bango abin jingina wajen cimma muradun PNGI.

ADVERTISEMENT

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ojulari ne bisa shirin da ya yi na yin gyara, tare da inganta shugabanci da jagorancin hukumomi da shugabannin na NNPC, domin samar da ci gaba mai inganci, tare da dawo da natsuwa a zukatan masu zuba jari, da kuma ƙara saita kamfanin a hanyar kasuwancin harkar albarkatun man fetur na ƙasa.

Don haka, Ojulari yana kama aiki sai ya tsunduma aiki, inda ya tsara sabuwar tawagar manyan shugabannin kamfanin, tsara fikirori, raba ayyuka, tare da sanya ido wajen tabbatar da samar da sakamako mai kyau da aka ɗora ma kowa.

LABARAI MASU NASABA

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ƙungiyar PNGI ta kuma bayyana cewa matakin farko, kuma mai muhimmanci da Ojulari ya fara a shugabancin sa, shi ne ƙarfafa dabarun haɗin gwiwa a hanyoyin matakin bincike da haƙo albarkatun mai, da fannin tattarawa, adanawa da jigilar albarkatun man, da kuma fannin tacewa, sarrafawa da rarrabawa, a matsayin fannoni masu muhimmanci.

Kamfanin NNPC ya samu sakamako mai kyau a fannin tacewa da gudanarwa, tare da samar da tabbaci mai natsuwa a tsakanin ma’aikata, ta hanyar ƙarfa haɗin gwiwa, dogaro da kai da kuma ayyukan ci gaba a wannan fanni mai mihimmanci.

A ƙarƙashin shugabancin Ojulari, NNPC ya samu nasarar samar da ganganar ɗanyen mai har 355,000 a kowace a shekarar 2025 daga kadarori da sauran hanyoyin ci gaban sashen. Waɗannan sun haɗa da ‘fist oil’ daga ‘Modu field’ da shirin Gyara don samun sakamako mai kyau na bututun mai na ‘Soku pipeline corridor,’ da na ‘Akpo West start-up’, tare da ƙaddamar da ‘Gbaran Nodal Compression Train,’ duk waɗannan sun taimaka wajen inganta dogaro da mafita mai kyau.

Sama da neman wani amfani na kurkusa, Olajuri ya fito da wasu hanyoyi masu dogon zango na samar da albarkatun mai, inda ake harin samar da gangar ɗanyen mai Miliyan 2 a kowace rana a shekarar 2027 mai zuwa, sannan ganga Miliyan 3 a kowace rana a shekarar 2030, ta hanyar zuba jari mai tsari da bin ƙa’ida, kare ingancin kadarori, da tabbatar da tsaro da ababen more rayuwa.

Batun samuwar bututun mai a koda yaushe da kuma kare kayan more rayuwa daga lalacewa ya kasance muhimmin bangare na ajandar gyaran da ake yi. PNGI na sane da cewa shugabancin na yanzu ya ba da fifiko wajen tabbatar da cewa bututun mai na aiki kusan kashi ɗari bisa ɗari domin rage asara da kuma daidaita kuɗaɗen shiga. A bangaren iskar gas kuwa, an jaddada ci gaban aikin bututun Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), ciki har da muhimmin sashen da ya ratsa Kogin Neja, a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa amfani da gas a cikin gida, tallafa wa masana’antu da kuma ƙarfafa tsaron makamashi.

A bangaren mai da ake sarrafawa, wato downstream, shugabancin Ojulari ya fara cikakken nazari na fasaha da kasuwanci kan kadarorin matatun mai na Nijeriya, domin tantance kimarsu, ɗorewarsu da zabukan da ke gaba. A cewar PNGI, wannan mataki na nuna sabuwar hanya ta kasuwanci mai ma’ana wajen tafiyar da kadarori. Haka kuma, an faɗaɗa ayyukan kamfanin NNPC a wannan bangare ta hanyar ƙaddamar da baƙin mai na Oleum a kasuwannin Afirka ta Yamma, alamar ƙoƙarin wuce iyakokin cikin gida.

Game da shugabanci, ƙumgiyar ta ce Ojulari ya dawo da kima da gaskiya a ayyukan kamfanin NNPC ta hanyar dawo da fitar da rahotannin kuɗi da na ayyuka kowane wata. Haka zalika, an amince da sabbin tsare-tsaren rabon iko (Delegation of Authority) domin fayyace nauyin aiki, rage jinkiri wajen yanke hukunci da kuma ƙarfafa tsarin duba ayyuka. PNGI ta ƙara da cewa, taƙaita kashe kuɗi da rage barnar dukiya sun zama ginshiƙi wajen mayar da NNPC kamfani mai neman riba bisa ƙa’idojin kasuwanci, ba wai tafiyar ofis kawai ba.

An kuma mai da hankali kan bunƙasa ma’aikata. Sanarwar ta ce, Ojulari ya yi ƙoƙarin kyautata walwalar ma’aikata, gyara gibi na tsofaffin haƙƙoƙi da kuma ƙarfafa al’adar aiki bisa nagarta. An ɗauki sabbin matasa ƙwararru da ake kira “Tigers”, domin gina sabbin shugabannin fannin makamashi na gaba da kuma kawo sabbin dabaru cikin kamfanin.

Baya ga mai da gas, mulkin Ojulari ya yi daidai da manufofin sauyin makamashi na ƙasa. PNGI ta ambaci tallafin NNPC na hanyoyin makamashi masu tsafta, ciki har da bayar da bas-bas 35 masu amfani da iskar gas ta CNG ga shirin Shugaban Kasa na CNG, a matsayin misalin daidaitaccen tsari tsakanin tsaron makamashi da kula da muhalli.

A bangaren kuɗi, PNGI ta ce NNPC ya ƙara yawan gudunmawar da yake bayarwa ga Asusun Tarayya ƙarkashin shugabancin na yanzu, alamar kyakkyawan sakamakon kasuwanci, taƙaita kashe kuɗi da ingantaccen tattara kuɗaɗen shiga. Kuɗaɗen kula da ayyuka da ribar binciken mai ma sun ƙaru, abin da ya ƙara ƙarfin tattalin arzikin kamfanin da gudunmawarsa ga ƙasa.

Ƙungiyar ta yaba da irin waɗannan nasarori, tana mai cewa Ojulari ya kasance abin koyi ga matasa wajen nagartaccen shugabanci. Ta ƙara da cewa, yana zaburar da matasan Nijeriya su bada tasu gudunmawar wajen gina ƙasa.

PNGI ta sake jaddada matsayinta a matsayin ƙungiya mai dogaro da bincike da bayanai wadda ke ƙarfafa sahihin shiga harkokin siyasa da riƙon amana a shugabanci. Ta kuma gode wa Ojulari bisa amincewa da zama jagoran ƙungiyar ‘Patron’, tana mai cewa hakan ya ƙara wa ƙungiyar karbuwa a faɗin ƙasa.

Yayin da Nijeriya ke tunkarar wani sabon zango PNGI ta yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da shugabanci na haɗin gwiwa bisa ajandar ‘Renewed Hope’.

Tun daga ranar 2 ga Afrilu, 2025, a cewar PNGI, shugabancin Ojulari ya ɗora NNPC a turbar bunƙasar samar da mai, ingantattun kayayyakin more rayuwa, rahoto a buɗe, tsari mai inganci, bunƙasar ma’aikata da kuma ƙarin gudunmawar kuɗi — duk alamu na sauyi da nufin sabunta babban kamfanin makamashi na Nijeriya domin ya dace da sauyin da duniya ke ciki.

NNPC
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
NNPC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa

MASU ALAKA

NNPC
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Next Post
Mahaifin Wilfred Ndidi Ya Rasu

Mahaifin Wilfred Ndidi Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

NNPC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.