ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 6, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago
APC

Ƙungiyar haɗakar jam’iyyun adawa mai suna Coalition for Democracy ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin taƙaita ƴancin siyasa da dimokuraɗiyya a Nijeriya, ta hanyar ƙirƙirar yanayin da zai bai wa jam’iyyar mai mulki fifiko tare da hana ƴan adawa gudanar da harkokinsu cikin ƴanci gabanin babban zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron kwamitin shugabanninta da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026. Ta kuma sanar da sauya sunanta daga G100 Coalition zuwa Coalition for Democracy, tana mai cewa manufarta ita ce kare kundin tsarin mulki, da bin doka da kuma haƙƙoƙin siyasa na ƴan Nijeriya.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa a cikin kwanaki 90 da suka gabata an kai hare-hare kan magoya bayan ƴan adawa a Kaduna, da Ibadan, da Sakkwato da Cross River. Ta kuma yi zargin cewa wasu otal-otal sun soke yarjejeniyar bai wa ƴan adawa wuraren gudanar da taro, an rufe wasu ofisoshin kamfen, an cire allunan tallan ƴan adawa a Jihar Edo, yayin da ake karɓar kuɗaɗe masu yawa daga jam’iyyun adawa domin tallan siyasa a Abuja.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, ƙungiyar ta nuna damuwa kan sahihancin kundin rajistar masu zaɓe na INEC, musamman bayan rahotannin gano hotunan da ake zargin an ƙirƙira da fasahar AI a cikin bayanan rajistar, da kuma cire bayanan rajista sama da miliyan 1.27. Ta buƙaci hukumar zaɓen ta gudanar da bincike mai zurfi kan kundin rajistar, ta wallafa sakamakon binciken kafin ranar 15 ga Disamba, tare da hukunta jami’an da aka samu da hannu wajen yin maguɗi.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci Sufeto-Janar na Ƴansanda, Tunji Disu, da ya tabbatar da tsaron dukkan jam’iyyun siyasa ba tare da nuna bambanci ba, tare da bayyana sakamakon binciken hare-haren da aka kai wa magoya bayan ƴan adawa.

LABARAI MASU NASABA

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

APC Na Son Jefa Nijeriya Cikin Rikici – ADC

Ta ce ya zama wajibi hukumomin gwamnati su tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa suna da damar gudanar da taruka da kamfen cikin ƴanci, domin bai wa ƴan Nijeriya damar zaɓar shugabanninsu yadda suke so.

APC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano
  • Abubakar Sulaiman
    ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Masu Amfani Da Moniepoint Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Na Gwamnatin Tarayya
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Masu Amfani Da OPay Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Kyauta Daga Gwamnati

MASU ALAKA

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC
Manyan Labarai

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

November 5, 2026
ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro
Manyan Labarai

APC Na Son Jefa Nijeriya Cikin Rikici – ADC

November 5, 2026
Shirin Atiku Na Dawo Da Tallafin Mai Zai Dawo Da Nijeriya Baya Da Shekaru 20 — TSG
Manyan Labarai

Atiku Ya Zargi APC Da Amfani Da Kotu Domin Raunana ADC

November 5, 2026
Next Post
Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

November 6, 2026
ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

November 6, 2026
Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

November 6, 2026
Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

November 6, 2026
Tallafin Tinubu: Cin Hanci Ko Taimako? Jam’iyyun Adawa Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Nuna Shakku

Tallafin Tinubu: Cin Hanci Ko Taimako? Jam’iyyun Adawa Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Nuna Shakku

November 6, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Jigon “Jagorancin Kasar Sin Da Ci Gaban Duniya” A Kuwait

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Jigon “Jagorancin Kasar Sin Da Ci Gaban Duniya” A Kuwait

November 5, 2026
Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

November 5, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

November 5, 2026
Wang Huning Ya Yi Kira Ga Mabiya Addinin Dao Su Ba Da Gudunmuwa Ga Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Dan Adam

Wang Huning Ya Yi Kira Ga Mabiya Addinin Dao Su Ba Da Gudunmuwa Ga Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Dan Adam

November 5, 2026
Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.