Da yammacin yau Alhamis 5 ga wata ne aka fitar da muhimmin rahoton dandalin tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao, mai taken “Rahoton bude kofar kasashe ga duniya na shekarar 2026”, wanda tuni ake fitarwa cikin shekaru 6 a jere.
Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2025, ma’aunin yanayin bude kofa na kasa da kasa ya yi raguwa mafi girma cikin shekaru 10 da suka gabata, amma ma’aunin bude kofa na kasashe da yankuna mafiya saurin bunkasar tattalin arziki dake cikin halin tasowa, ya karu idan an kwatanta da makamancin lokaci na shekarar da ta gabace ta, daga cikinsu Sin tana sahun gaba tsakanin kasashe masu tasowa wajen bude kofarta ga ketare.
Bugu da kari, dandalin tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao karo na 9, ya fitar da “Rahoton ci gaban karfin fitar da kayayyaki zuwa Sin” a yau. Rahoton ya yi bayani kan damammakin babbar kasuwar Sin ta kowane fanni, bisa tsarin shigo da kayayyaki, masu cinikayya, bukatun kasuwa da tsare-tsare da manufofi, sannan ya nazarci wasu abokan hulda da tsarin fitar da kayayyakinsu, da kuma yadda kayayyakinsu suka biya bukatun kasuwar Sin, inda ya ba da shawarwari kan yadda za su bunkasa karfin fitar da kayayyaki zuwa Sin.(Amina Xu)














