ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan El-Rufai Ya Zargi ICPC Da Hana Mahaifinsa Ganin Likita Ko Iyalansa

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Mohammed Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi ICPC da hana mahaifinsa damar ganin likitansa da kuma iyalansa yayin da yake tsare a hannun hukumar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Bello ya ce jami’an ICPC sun hana likitan mahaifinsa ganinsa duk da umarnin kotu da ya ba shi damar samun kulawar lafiya ba tare da takura ba. Ya ce likitan ya kai ziyara ofishin ICPC da misalin ƙarfe 3 na rana domin tattauna sakamakon gwaje-gwajen lafiya da aka yi wa tsohon gwamnan, amma aka hana shi shiga saboda wai sai shugaban ICPC ya bayar da izini.

Ya kuma yi zargin cewa matar El-Rufai, Aishatou El-Rufai, an hana ta shiga bayan ta kai masa abincin dare da misalin ƙarfe 7 na yamma, inda jami’an suka ce an hana karɓar abinci bayan ƙarfe 6:30 na yamma.

ADVERTISEMENT

“Har yanzu ana tsare da mahaifinmu, Mallam Nasir El-Rufai, a hannun ICPC,” in ji Bello, yana mai bayyana matakin a matsayin “cin zarafin dokar ƙasa kai tsaye.” Ya ce babu wani dalilin doka da zai sa a hana wanda ake tsare da shi ganin likita ko samun ganawa da iyalansa.

Ƙoƙarin jin ta bakin ICPC bai yi nasara ba kafin kammala wannan rahoto. Ana tuhumar El-Rufai ne da zargin almundahanar kuɗi da kuma sakin biliyoyin naira domin aiyukan da ake zargin ba a aiwatar da su ba, zarge-zargen da ya musanta.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

MASU ALAKA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”
Manyan Labarai

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Next Post
CAF

Nijeriya Za Ta Karbi Bakuncin Babban Taron Hukumar CAF Na Bana

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

July 14, 2026
Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.