ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Za Ta Karbi Bakuncin Babban Taron Hukumar CAF Na Bana

by Abba Ibrahim Wada
4 months ago
CAF

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya amince da bukatar karbar bakuncin Babban Taron Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirika mai dauke da kasashe 54 wanda kuma ya hada da bikin bayar da kyaututtuka na CAF na shekarar 2026, an tabbatar da amincewar ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya, Ademola Olajire ya fitar, a cewar sanarwar Shugaban ya sanar da amincewar ne a lokacin taron kasashen Afrika da aka gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya, bayan haduwa da Shugaban CAF Patrice Motsepe.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministar Harkokin Waje ta Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya, Ibrahim Musa Gusau, Babban mai bayar da shawara na Musamman ga Shugaban CAF, Amaju Melbin Pinnick, da kuma Mukaddashin Sakatare Janar na CAF, Samson Adamu.

Babban taron CAF karo na 48, wanda aka shirya gudanarwa a watan Oktoba, zai tattaro manyan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa ta Afirka, ciki har da shugabannin kungiyoyin CAF guda 54, wakilan shiyyoyi 6 na CAF da kuma sauran masu gudanar da kwallon kafa, da manyan jami’ai daga fadin nahiyar.

ADVERTISEMENT

Ana daukar taron a matsayin daya daga cikin muhimman taruka a kwallon kafa ta Afirka, inda ake tattaunawa da amincewa da manyan shawarwari game da ci gaba da gudanar da wasan kwallon kafa a nahiyar Afirika, nasarar da Nijeriya ta samu na karbar bakuncin taron ya kara nuna tasirin da kasar ke da shi a cikin harkokin kwallon kafa ta Afirka.

Baya ga taron, Nijeriya za ta kuma karbi bakuncin bikin bayar da kyaututtuka na CAF, daya daga cikin manyan taruka da hukumar ta CAF ke Shiryawa a kowace shekara inda ake zabo zakakurai a fannoni da dama na kwallon kafa domin karramasu, bikin na shekara-shekara yana zakulo fitattun yan wasa a kwallon kafa ta Afirka, ciki har da yan wasa, masu horarwa, kungiyoyin kwallon kafa da masu gudanar da kwallon kafa wanda manyan yan wasan kwallon kafa na Duniya da manyan mutane suka halarta.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Masu ruwa da tsaki a harkar wasanni a Nijeriya sun bayyana nasarar a matsayin babban ci gaba da Nijeriya ta samu wanda zai sake janyo masu zuba jari a harkar kwallon kafa tare da tsammanin cewa abubuwan da za su faru za su jawo hankalin kasashen Duniya da kuma karfafa ayyukan tattalin arziki a cikin birnin Abuja Wanda shine mai masaukin baki, amincewar ta kuma nuna dangantakar dake tsakanin hukumomin kwallon kafa na Nijeriya da shugabancin CAF a karkashin Motsepe.

CAF
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
A Karon Farko Mahajjatan Zamfara Sun Tashi Daga Jiharsu

A Karon Farko Mahajjatan Zamfara Sun Tashi Daga Jiharsu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.