ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan Takarar Gwamnan NNPP A Katsina Zai Kawar Da Ƙazantar APC Da PDP – Hajiya Farida Barau

by yahuzajere
4 years ago
nnpp

Uwargidan ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar NNPP, Engr Nura Khalil, wato Hajiya Farida Muhammad Barau ta bayyana cewa duk mutanen da ke cikin jam’iyyar NNPP mutanen kirki ne da ba su taɓa ɗaukar alhakin kowa a siyasa ba.

Uwargidan ɗan takarar rar ta bayyana hakan ne a ofishin yaƙin neman zaɓen maigidan nata da ke kan titin IBB Way cikin birnin Katsina, lokacin da ta ƙaddamar da muhimman manufofin takararsa ga matan jihar Katsina.

Hajiya Farida Muhammad Barau ta yi bayanin cewa ce; “Lema ta yage, tsintsiya ta watse, an ɗora mana yunwar dole, an sa mana talauci, mai cin abinci sau uku yanzun ma babu, an maida mu jawarawa, an kashe mana mazajenmu, an sace mana mata, shin wai haka za mu zauna ne?

ADVERTISEMENT

“Mun zama shanaye an maida mu awakai, wannan Jam’iyya ta NNPP jaririya ce ba ta da hakkin kowa wallahi, mutanen duk da kuka gani cikin wannan jam’iyar mutanen kirki ne. Engr Muhammad Nura Khalil ya daɗe yana taimako, mai tausayi ne da kuɗinsa yake amfani yake fiddawa ya ba da, bai taɓa riƙe ko kansila ba, amma ya san hanyar da ake neman kuɗi, kuma a cikinsa yake ɗiba yake taimakon mutane.

“Shin ina ga ya samu wata dama wadda zai taimake ku da kuɗinku? Mine ne ba zai maku ba? Bai iya cin haƙƙin mutane ba, bai taɓa aikin gwamnati ba, bai taɓa ciyar da iyalinsa da haramun ba, bugu da ƙari ga shi yana da tausayin mata da ƙananan yara da matasa.” In ji Hajiya Farida.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

  • Da Dumi-dumi: Gwamnan Gombe Ya Rushe Shugabannin Kananan Hukumomin Bayan Karewar Wa’adin Mulkinsu

Har ila yau, shi ma a nasa jawabin, ɗan takarar gwamnan na NNPP a Jihar Katsina, Engr Muhammad Nura Khalil ya bayyana cewa idan ya lashe zaɓen jihar matan Katsina za su ji daɗi sosai, inda ya ƙara da cewa duk wata sai ya tallafi matan jihar Katsina dubu talatin da huɗu da kayan tallafi kuma har ya kammala wa’adinsa ba zai daina ba.

NNPP

Haka zalika da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban jam’iyyar NNPP ta Jihar katsina Honorable Sani Liti Yankwani ya yaba ma uwargidan dantakarar gwamnan a bisa ƙoƙarin da take na ganin maigidanta ya samu nasara da ma jam’iyya baki ɗaya, a zaɓe mai zuwa na 2023.

Ya ƙara da cewa babu shakka duk inda ka ga namiji ya samu nasara to za ka same shi da mace irin Hajiya Farida Muhammad Barau a tare da shi domin ita mace ce mai nagarta da kuma sanin ya kamata, “kazalika idan ba ka zauna da Farida ba ba za ka san wace ce Farida ba domin mace ce mai son ganin ci gaban Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.”
Shi ma a nasa jawabin, Kwamrad Bashir Bala Funtua, ɗaya daga cikin matasan da ke dafa wa ɗan takarar na NNPP, Engr Nura Khalil baya wajen fafutukar jawo matasa don mara masa, ya bayyana cewa “ka da wata mace a Jihar Katsina ta yarda wasu ‘yan siyasa su ba su ‘yan kudi ƙalilan don zaɓar su, su tsaya su dubi cancanta su mara wa Engr Nura Khalil baya don samun kyakkyawan shugabanci a jihar Katsina.” In ji shi

 

nnpp
yahuzajere
+ postsBio
  • yahuzajere
    Da Kujerar Mulki Gara Zaman Lafiyar Kano
  • yahuzajere
    Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya
  • yahuzajere
    Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
  • yahuzajere
    Sin Ta Kaddamar Da Gagarumin Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Kasar Sin

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
nnpp
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Yarjejeniyar Kare Mabambanta Hallitu a Duniya Ta Kunming Da Montreal Ta Fidda Wata Hanya Mai Dacewa a Fannin Kare Hallitu

Yarjejeniyar Kare Mabambanta Hallitu a Duniya Ta Kunming Da Montreal Ta Fidda Wata Hanya Mai Dacewa a Fannin Kare Hallitu

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.