ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wanene Alhaji Ibrahim Galadima Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Nijeriya

by Rabilu Sanusi Bena
5 months ago

Magoya bayan kwallon kafa a Nijeriya na cigaba da jimamin rashin daya daga cikin fitattun mutane a fagen kwallon kafa a Nijeriya, Alhaji Ibrahim Galadima, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFA), wadda yanzu aka fi sani da (NFF), Alhaji Galadima ya rasu a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilun shekarar 2026, a Kano, yana da shekaru 74.

Alhaji Sani Ahmed Toro, tsohon Sakatare Janar na hukumar NFA, wanda ya yi aiki tare da Galadima a lokacin baya ne ya tabbatar da labarin rasuwarsa, Toro, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “Ina matukar bakin ciki da sanar da mutuwar Alh Ibrahim Galadima, tsohon Shugaban NFA, a yau a Kano, Allah ya saka masa da Aljanna Firdausi”.

  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

An haifi Alhaji Galadima a ranar 14 ga watan Yunin 1951, a karamar hukumar Fagge dake Kano, ya shafe muhimmin lokacin rayuwarsa wajen ganin ci gaban wasanni a Nijeriya, musamman kwallon kafa, ya shugabanci hukumar kwallon kafa ta jihar jihar Kano tsakanin shekarun 1977 da 1979, ya cigaba da aikinsa a ma’aikatar wasanni bayan ya zama shugaban Gudanarwa na Majalisar Wasanni ta Jihar Kano daga shekarar 1981 zuwa 1983.

ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya a wancan lokacin ta bukaci yayi aiki da ita a matakin kasa, wanda hakan ya sa aka nada shi memba na Kwamitin Kula da Wasanni na Hukumar Wasanni ta kasa a shekarar 1983, tasirin Galadima ba a iya kwallon kafa kawai ta tsaya ba bayan ya zama mataimakin shugaban kwamitin Olympics na Nijeriya (NOC) a shekarar 1985, kujerar da ya rike har zuwa shekarar 1987.

Galadima ya taba zama Kwamishinan Jin Daɗin Jama’a, Matasa da Wasanni a shekarar 1989, daga baya kuma ya zama Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri, ya kuma kasance memba na Kwamitin Kula da Shugaban Kasa kan bunkasa filayen wasa na Gasar Cin Kofin Matasan Duniya ta FIFA da Nijeriya ta karbi bakunci a shekarar 1995, gasar da daga karshe aka mayar da ita Qatar saboda barkewar cutar sankarau a wani yanki na Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Alhaji Galadima ya sake zama memba na Kwamitin Gasar Matasa na CAF. A shekarar 1999, ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da ya rike shugaban kwamitin wasanni na jihar Kano a Gasar Cin Kofin Matasa ta FIFA a Nijeriya a shekarar 1999, babbar nasarar da ya samu a harkokin kwallon kafa ta zo ne a shekarar 2002 lokacin da aka zabe shi Shugaban hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya a wancan lokacin.

Ya jagoranci hukumar har zuwa shekarar 2006, inda ya bar tarihi mai kyau a tsawon shekaru 4 da yayi a saman kujerar, bayan rawar da ya taka a matakin kasa, ya kuma koma Kano domin yin aiki a matsayin shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars, daga baya kuma ya zama shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayinsa a matsayin babban mutum a bangaren wasanni a Nijeriya, mutuwar Alhaji Ibrahim Galadima ta bar wani babban gibi a harkar kwallon kafa ta Nijeriya wanda za a shafe tsawon lokaci ana tunawa dashi, amma kuma tarihin da ya bari ba zai taba goguwa a zukatan masoya harkar kwallon kafa a kasar ba.

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Ahanor Kan Fam Miliyan 40

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Mutum-Mutumin Inji Na Sin Ya Cimma Saurin Dan Adam A Gasar Tseren Rabin Dogon Zango

Mutum-Mutumin Inji Na Sin Ya Cimma Saurin Dan Adam A Gasar Tseren Rabin Dogon Zango

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.