Jam’iyyar ADC ta yi gargadi kan abin da ta bayyana a matsayin yadda gwamnatocin da ke kan mulki, da kuma masu faɗa-aji, ke kara cin zarafin tsarin zaɓen Nijeriya gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark, ne ya bayyana damuwar a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar wata tawaga daga Cibiyar International Republican Institute (IRI), ƙarkashin jagorancin Daraktar yankin Afirka, Jenai Cox.
Mark ya ce dole ne sahihancin babban zaɓen 2027 ya zama zaɓin ‘yan Nijeriya ne ba na sayarwa ba, yana mai jaddada buƙatar samar da tsarin zaɓe na gaskiya, mai haɗa kowa da kowa, kuma cikin lumana, ba tare da maguɗi, barazana ko amfani da hukumomin gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba ba.
Ya ce, “Muna matukar damuwa kan yadda gwamnatocin da ke kan mulki, da kuma masu faɗa-aji, ke cin zarafin tsarin zabe.”
Ya yi Allah-wadai da tashin hankali da barazanar da aka gani yayin zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka kammala kwanan nan, inda ya ce rahotanni sun nuna cewa, a ƙalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a yayin zaɓen.
A cewarsa, bai kamata a ḍauki zaɓe a matsayin yaki ko wani abu na dole sai an yi nasara ba, domin zaɓe tsari ne na dimokuraɗiyya da ke bai wa ‘yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci tare da cimma burinsu na ci gaba da inganta rayuwa.














