Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana alƙawarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur a matsayin dabarar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Fayemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.
Ya kwatanta batun tallafin man fetur na Atiku da tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC ta yi amfani da shi a zaɓen 2023.
A cewar Fayemi, wannan alƙawari na iya samun karɓuwa a wajen ’yan Nijeriya da ke fama da wahalhalun da cire tallafin man fetur ya haifar.
Ya ce, “Ra’ayina shi ne, shawarar Atiku kan tallafin man fetur ta yi kama da tikitin Musulmi da Musulmi da muka yi amfani da shi a 2023. Dabara ce ta siyasa, ba tsarin tattalin arziƙi ba.”
Fayemi ya ce har yanzu yana goyon bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa ya daɗe yana kira da a cire shi tun lokacin da yake shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya.
Sai dai ya soki yadda Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar da cire tallafin, yana cewa gwamnatin da ta gabata ta riga ta kammala wasu muhimman shirye-shiryen cire tallafin.
Fayemi ya ce gwamnonin jihohi sun kuma yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya wajen samar da matakan rage wa talakawa raɗaɗin cire tallafin.
Ya ce yawancin ’yan Nijeriya ba su damu da bayanan cire tallafin ba, illa dai suna son samun damar sayen kayan abinci, lafiya da tura ’ya’yansu makaranta.
Fayemi ya ƙara da cewa talauci da rashin daidaito a tsakanin al’umma na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar tsaro, ciki har da ta’addanci da ’yan bindiga.
Ya ce Atiku na ƙoƙarin samun goyon baya ta hanyar amfani da wahalhalun da cire tallafin man fetur ya jefa ’yan Nijeriya a ciki.














