Cacar baki ta kaure tsakanin jam’iyyar APC da jam’iyyun adawa kan tallafin gwamnatin tarayya ga magidanta na dala biliyan 1, inda jam’iyyun adawa ke zargin cewa wannan shirin an tsara shi ne don ya yi tasiri kan masu kada kuri’a kafin zaben 2027.
Jam’iyyun adawa, ciki har da ADC da NDC, sun saka ayar tambaya kan lokacin shirin, wanda aka kaddamar a Abuja a ranar Laraba a yayin da ayyukan siyasa ke kara karuwa kafin zabe.
Duk da haka, APC ta yi watsi da zargin, tana jaddada cewa wannan yunkurin na gaskiya ne daga gwamnatin Bola Tinubu don yaki da talauci da samar da tallafin tattalin arziki mai dorewa ga ‘yan Nijeriya masu rauni.
Gwamnatin tarayya ta ce an tsara shirin ne don bayar da tallafi na gajeran lokaci ga al’ummar Nijeriya wajen karfafa tattalin arziki da dogaro da kai mai dorewa.
Wannan shirin yana nufin taimaka wa magidanta masu rauni ta hanyar gano abin da zai amfane su, bayar da tallafin gaggawa a lokacin da ake ciki kuncin tattalin arziki da kirkirar hanyoyi don magidanta su fita daga talauci.
An kaddamar da shirin ne ta hannun uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, wacce ta ce sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnatin Tinubu za su ci gaba da tallafa wa ‘yan Nijeriya masu rauni.
“A karkashin jagorancin Mai Girma, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, kasarmu na aiwatar da manyan sauye-sauye don karfafa tattalin arziki, gina turbayar ci gaba da kuma raba arziki,” in ji ta.
Ta kara da cewa magidanta da dama suna ci gaba da fuskantar matsaloli duk da gyare-gyaren da ake yi, tana mai jaddada cewa shirin zai samar da tallafin daidaitawa nan take, yayin da zai dora magidanta masu rauni kan hanyar murmurewa da samun dogaro da kai.
Gwamnatin tarayya ta ce shirin zai tallafa wa magidanta masu rauni kusan miliyan 7.6, inda ake sa ran wadanda za su amfana da shirin kowannensu zai samu naira 40,000. Za a zabi masu cin gajiyar Shirin ta hanyar musu rajista ta katin shaidar dan kasa.
Ministan al’amuran jin kai da rage radadin talauci, Dakta Bernard Doro, ya ce gwamnati na tallafa wa marasa karfi ta hanyoyi daban-daban.
Ya bayyana cewa an raba sama da naira biliyan 600 a cikin ga ‘yan Nijeriya masu rauni a cikin shekaru uku da suka gabata, wanda ya kai fiye da magidanta miliyan 10 sun amfana da shirin.
Sai dai jam’iyyun adawa sun ce akwai ayar tambaya ka wannan sabon tallafin, musamman ganin cewa za a yi zaben 2027 kasa da shekara guda.
Jam’iyyar ADC ta bayyana shirin na dala biliyan 1 a matsayin martani ga wahalhalun tattalin arziki da ‘yan Nijeriya suka fuskanta a karkashin gwamnatin Tinubu, kuma ta danganta kaddamar da shirin da karuwar wata ukuba ga ‘yan Nijeriya, wanda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, yana da shirin dawo da tallafin idan aka zabe shi a matsayin shugaban.
A cikin wata sanarwa da sakatare jam’iyyar kan harkokin yada labarai, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta jefa ayar tamba kan dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ke yin manyan alkawurikan bayar da tallafin kudi bayan da ‘yan Nijeriya suka dade suna korafe-korafe kan hauhawar farashin kayayyakin abinci da sufuri da kuma makamashi.
Jam’iyyar ta ce a baya gwamnatin tarayya ta ce ba ta da kudin da za ta kashe don rage tasirin gyaran tattalin arzikinta yadda ya kamata, amma yanzu ta samu dala biliyan 1 don kaddamar da tallafi a yayin da zabe ke karatowa.
ADC ta ce tana goyon bayan kokarin tallafa wa ‘yan Nijeriya masu rauni, amma ta bayyana cewa tallafin ba zai maye gurbin tasirin mummunar manufofin gwamnati da ta jefa ‘yan Nijeriya cikin kuncin tattalin arziki ba.
Har ila yau, ta zargi gwamnati da kokarin magance mummunar manufofin tattalin arzikinta ta hanyar siyasantar da tallafin gabanin zaben 2027.
Haka kuma, jam’iyyar NDC ta ce tana maraba da kowane mataki na gaskiya da nufin inganta walwalar ‘yan Nijeriya amma akwai ayartambaya katan wannan lokacin da aka kaddamar da shirin tallafin.
Sakataren yada labaran jam’iyyar, Osa Director, ya shaida wa wakilinmu cewa kusancin sabada zabe ne gwamnatin tarayya ke kokarin bayar da tallafi.
“Muna maraba da kowace hanyar da aka dauka don magance kalubalen da ke fuskantar mutanenmu. Duk da haka, ganin cewa zabe na karatowa ne, mutum na iya mamakin dalilin da ya sa gwamnati ta dauki wannan mataki a yanzu.
“Lokaci zai tabbatar domin akwai ayar tambaya da jam’iyya mai mulki da gwamnati za su kasa amsawa,” in ji shi.
A nata bangaren, jam’iyyar SDP ta yi tsokaci kai tsaye kan wannan tallafi, tana bayyana wannan shiri a matsayin dabarar jan hankalin masu kada kuri’a kafin zabe.
Mai magana da yawun jam’iyya, Rufus Aiyenigba, ya shaida wa ‘yan jarida cewa wannan matakin yana nufin shirin neman kuri’u daga wurin magidanta, ko da yake ya kara da cewa irin wannan yunkurin ba zai iya tabbatar da nasara a zabe ba.
Sukan ‘yan adawa ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin kare matakinta bayan cire tallafin man fetur da hade kasuwar canjin kudaden waje da manufofi da gwamnati ta saba karewa a matsayin wajibi don farfadowar tattalin arziki.
Gwamnati ta tabbatar da cewa sabon tsarin zai taimaka wa ‘yan Nijeriya masu Rauni, yayin da ta dauki alkawarin aiwatarwa da shirye-shiryen ci gaba da gyare-gyaren tattalin arziki.
Sai dai kum jam’iyyar APC mai mulki ta karyata zargin da ‘yan adawa suka yi, mai cewa kasancewar zabukan 2027 na kusantowa ba yana nufin gwamnati ta dakatar da ayyukanta ga ‘yan Nijeriya ba.
Daraktan yada labaran jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce gwamnatin tarayya na da ikon ci gaba da aiwatar da shirye-shirye da aka tsara don inganta jin dadin ‘yan kasa ba tare da la’akari da jadawalin zabe ba.
“Saboda zabe na zuwa ba yana nufin gwamnati ta kau da kai daga ayyukanta. Ya kamata ta ci gaba,” in ji Ibrahim.
Mai magana da yawun APC ya ce shirin tallafin gwamnatin tarayya na gudana tun kafin lokacin zaben 2027, kuma ka da a dauki aiwatarwarsa a matsayin na siyasa kawai.














