Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta sake fasalin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ta bai wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, muhimman muƙamai.
A sabon tsarin, an naɗa Wike a matsayin mai kula da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu a Jihar Rivers da Babban Birnin Tarayya, Abuja, yayin da Adeleke zai jagoranci ayyukan yaƙin neman zaɓen a Jihar Osun.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, zai riƙe muƙamin daraktan kuɗi na kwamitin.
An kuma ɗora wa Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, da Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, alhakin kula da tattara kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen.
Sauye-sauyen na zuwa ne gabanin bikin rantsar da mambobin kwamitin, wanda aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, a zauren Banquet Hall da ke fadar shugaban ƙasa an Abuja.














