Muhammad Wani jigo a jam’iyyar APC, Yusuf Dingyadi, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu aƙalla kashi 80 na ƙuri’un da za a kaɗa a Jihar Sakkwato a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Dingyadi, wanda shi ne babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a garin Dundaye, hedikwatar gundumar Dundaye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko a Jihar Sakkwato.
Ya yi wannan furuci ne yayin wani shirin tallafa wa mutane 300 da ke cikin buƙata, wanda Manajan Daraktan Kamfanin Yaɗa Labarai na Jihar Sakkwato (SSMC), Labaran Lumo Dundaye, ya shirya.
Dingyadi ya ce APC tana da yakinin lashe zaɓukan shugaban ƙasa, gwamna, majalisun tarayya da kuma Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato.
Ya kuma yi hasashen cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a yankin Arewa maso Yamma, inda ya yi iƙirarin cewa yankin na da ƙuri’u sama da miliyan 20, kuma APC na fatan samun aƙalla miliyan 15 daga cikinsu.
A cewarsa, jam’iyyar ta fara shirye-shiryen zaɓen ta hanyar kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓe daga matakin mazabu har zuwa matakin shiyya.
Dingyadi ya kuma bayyana cewa za a ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Kaduna ranar 24 ga Oktoba.
Ya yaba wa Labaran Lumo Dundaye bisa tallafin kuɗi da ya bai wa mutane 300 daga yankunan Dundaye, Gumburawa da Gidan Bubu, yana mai cewa irin wannan taimako na daga cikin ayyukan da ya kamata shugabanni su riƙa yi wa al’ummominsu.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su taimaka wa gwamnati wajen inganta rayuwar jama’a da samar da muhimman abubuwan more rayuwa.














