Jam’iyyar APC ta ce ba za ta mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ta hanyar musayar kalamai ba, inda ta ce za ta mayar da hankali kan manufofi da nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta bi tafarkin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ba, inda ta jaddada cewa za ta mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ’yan Nijeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Majalisar ta bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan abin da ta kira rashin ladabi da kuma rashin girmama matsayin Shugaba Bola Tinubu, bayan Atiku ya kira shugaban ƙasar da sunansa na farko, wato “Bola”.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun majalisar yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake, ya ce sun lura da martanin da jama’a suka yi kan lamarin.
Alake ya bayyana cewa ana sa ran tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma mai neman kujerar shugabancin ƙasa zai nuna ladabi da kamun kai tare da girmama hukumomin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ce abin damuwa ne yadda Atiku, wanda sanarwar ta bayyana a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya gaza cika waɗannan ƙa’idoji ta hanyar kiran shugaban ƙasa da “Bola”.
A cewarsa, Atiku ya bari ƙiyayyar siyasa da abin da ya kira kwaɗayin mulki marar iyaka sun rinjayi ɗabi’ar dattijantaka da ake sa ran zai nuna tun bayan rashin nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.
Alake ya ce Atiku ya gaza zama abin koyi mai kyau ga matasa ’yan siyasa wajen nuna ɗabi’a nagari a harkokin siyasa.
Sai dai majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ce ta buƙaci shugabanninta, masu magana da yawunta, mambobinta da ƙungiyoyin magoya bayanta da su ci gaba da girmama Atiku tare da nuna masa ladabi da mutuncin da ya dace da tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa.
Alake ya ce jam’iyyar ba za ta rama abin da ta ɗauka a matsayin rashin girmama ofishin shugaban ƙasa ta hanyar yin irin hakan ga ɗan siyasar adawa ba.
Ya ce: “A matsayinta na jam’iyyar da ta ginu a kan akidun ci gaba da al’adun Afirka na girmamawa, majalisar yaƙin neman zaɓenmu ba za ta bi tafarkin Alhaji Atiku ba.”
Majalisar ta jaddada cewa za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya maimakon kai wa abokan hamayyar siyasa hari ko shiga musayar kalamai da su.
A cewar sanarwar, APC za ta gabatar da shirye-shiryenta ga ’yan Najeriya, ta bayyana nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu a mulkinsa, tare da fayyace yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin sauya yanayin tattalin arzikin ƙasar daga matakan gyare-gyare zuwa wadata.
Alake ya ce yaƙin neman zaɓen zai mayar da hankali kan bayyana ayyukan gwamnatin Tinubu yayin da yake neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Majalisar ta kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da magoya bayanta da su ci gaba da girmama abokan hamayyarsu na siyasa duk da bambancin ra’ayoyi kan ɗabi’arsu ko kalaman da suke furtawa.














