Farfajiyar siyasar Nijeriya na fuskantar sabuwar taƙaddama a yayin da masu ruwa da tsaki a zaɓen 2027 suka ƙara matsa lamba kan Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Joash Amupitan da ya yi murabus a bisa ga zarge- zargen nuna son kai, tsoma baki a harkokin jam’iyyu da kuma rashin amincewar jama’a ga jagorancinsa a zaɓen 2027.
Babbar jam’iyyar adawa ta ADC wadda ta gudanar da babban taron ta na ƙasa kashi na takwas a Abuja a ranar Talata tare da zaɓen Daɓid Mark a matsayin shugaba ta bayyana cewar ta gudanar da taron ne duk da son rai da hukumar zaɓe ta nuna na rashin sa ido a zaɓen a bisa ga fassara umurnin kotu a bisa ga zaɓin ran ta.
- Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
- Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
- Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
- Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
- Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus
Cece- kucen neman tsige shugaban hukumar zaɓen ya samo asali ne tun bayan naɗin da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe a inda waɗanda lamarin ya shafa suka haɗu a kan Amupitan a kan kujerar babu tabbacin gudanar da sahihin zaɓe a Nijeriya.
A ranar Asabar ɗin makon jiya jam’iyyar ADC ta sake sabunta kiran ta na cire shugaban hukumar zaɓen daga kujerarsa kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa Bolaji Abdullahi ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar cewar jam’iyyar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira bayyanar tsoffin saƙonnin nuna ɓangaranci a kafar sadarwa ta Ɗ da ake dangantawa da shugaban hukumar.
Kakakin jam’iyyar ya ce hakan babbar barazana ce ga sahihancin zaɓe a Nijeriya don haka jam’iyyar za ta ci- gaba gaba da matsin lamba har sai shugaban hukumar ya yi murabus, haka ma ya yi gargaɗin cewar ADC za ta iya ƙara ƙaukar matakin zanga-zangar lumana da rashin biyayya ga hukumomi idan ba a karɓi buƙatar su ba.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a wannan makon gamayyar ƙungiyar Ƴan Majalisar Wakilai a ƙarƙashin babbar jam’iyyar adawa ta ADC sun bayyana cewar Nijeriya da al’ummar ta na da tabbacin ba za su samu adalci ba a hukumar zaɓe a ƙarƙashin Amupitan.
Babban abin da ya ƙara rura wutar buƙatar tsige shugaban hukumar daga muƙaminsa shine tsofaffin saƙonnin da ake zargin ya wallafa a shafinsa na Ɗ waɗanda ke nuna goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki da Shugaba Tiinubu
A kan wannan ƙungiyar ƴan majalisar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta saukar da shugaban hukumar tare da gurfanar da shi a bisa zargin nuna son kai gabanin babban zaɓen 2027.
Jagoran ƙungiyar, Honarabul Afam Ogene ne ya bayyana matsayar ƴan majalisar bayan wani taron da suka gudanar a Abuja a ranar Litinin domin bayyana matsayarsu kan hayagar da ta ɗauki hankalin al’umma.
Ogene ya ce sabbin matakai da kuma kalaman da ake dangantawa da Amupitan sun jefa shakku kan ikon sa na kasancewa a tsaka- tsaki wajen gudanar da sahihin zaɓen ƙasar da ke tafe.
Ƙungiyar ƴan majalisar ta nuna damuwa kan rashin zama tsaka- tsaki da rashin nuna adalci daga shugaban hukumar wajen jagorantar zaɓen 2027 cikin gaskiya da sahihanci.
Ya ce ɗaukar matakin da suka yi ya biyo bayan wasu kalamai da ayyuka na baya- bayan nan da ake ganin sun nuna son kai da rashin daidaito ga shugaban hukumar
A kwanan baya ma dai kakkausan kiran murabus ɗin shugaban hukumar ya ƙara ƙamari ne daga manyan shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta ADC waɗanda suka buƙaci Amupitan ya yi murabus nan take a wani taro da suka gudanar a Abuja.
A kakkausan kalamansa a makon jiya, shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Daɓid Mark ya zargi shugaban INEC da ɗaukar matakai da ka iya kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa matakai da dama da hukumar ta ɗauka musamman a kan rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar na nuna tsantsar ɓangaranci fiye da kima wanda bai kamata shugaban hukumar zaɓe da ɗaukar ɓangare na.
A ta bakin shugabannin ADC, Amupitan ba zai iya gudanar da sahihin zaɓe mai cike da gaskiya da adalci ba ba a 2027 don haka suka yi gargaɗin cewa ci- gaba da zamansa na iya kai ƙasar nan ga tsarin jam’iyya ɗaya tilo.
Haka kuma a wata zanga- zangar lumana da suka gudanar a hedikwatar Hukumar Zaɓe a Abuja, jam’iyyar ta sake jaddada buƙatar nunawa shugaban hukumar ƙofar fita daga shugabancin hukumar, tana mai cewa hukumar zaɓe ta ƙetare iyakokin aikinta ta hanyar shiga fassarar hukuncin kotu maimakon barin aikin ga ɓangaren shari’a.
Lamarin ya ƙara daukar zafi ne bayan ƙungiyar masu shata dokokin jam’iyyar ADC suka haɗu a inuwa ɗaya tare da aminta da ƙudurin buƙatar sauke Amupitan tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya.
A cewar jagoran ƙungiyar Afam Ogene, shugaban INEC ya rasa amincewar manyan ƴan siyasa da al’ummar ƙasa a kan ba zai iya tabbatar da sahihin zaɓe ba.
Ƴan majalisar sun nuna damuwa kan zargin cewa Amupitan a baya ya taɓa bayyana ra’ayinsa kan siyasa a shafukan sada zumunta don haka ko kaɗan bai cancanta wanda ya ta’allaka kansa da wata jam’iyya ya shugabanci hukumar zaɓe ba.
A cewarsu irin waɗannan abubuwa na haifar da tambayoyi kan gaskiya, riƙon amana da sahihancinsa wajen jagorantar zaɓen gaskiya a Nijeriya.
Haka ma ƴan majalisar sun kuma yi gargaɗin cewar ci-gaba da wannan rikici zai iya ƙara raunana amincewar jama’a ga hukumar zaɓe don haka babu wata mafita face shugaban ya sauka daga jagorancin hukumar.
A cewarsu karkatar da shugaban hukumar zaɓen ya yi, ya jefa shakku kan zamansa tsaka- tsaki wajen gudanar da zaɓe lamarin da tuni hukumar zaɓe ta musamta cewar ba asusun shugabanta ba ne.
A martanin hukumar zaɓen ta sa ƙafa ta yi watsi da kiran murabus ɗin shugaban ta na cewar zarge-zargen da ake yi masa ba su da tushe ballantana makama don haka a yi watsi da su.
A ta bakin mai magana da yawun hukumar, Rotimi Oyekanmi ya bayyana cewa dukkan zarge-zargen ƙiirƙirarru ne da ba su da wata hujja. Haka ma hukumar ta jaddada ƴancin ta na cin gashin kai kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba ta dama ta hanyar bayyana cewar shugaban ta ba ya aiki a ƙarƙashin ko wace jam’iyya.
Hukumar ta kuma bayyana cewar matakin da ta ɗauka kan rikita- rikitar da ta dabaibaye jam’iyyar ADC ya biyo ne a bisa ga umurnin kotu ba wai mataki ne da ta ɗauka a ƙashin kai ba.
A kan taƙaddamar saƙonnin da ake yaɗa cewar shugaban hukumar ne ya wallafa a shafin Ɗ, hukumar zaɓen ta yi watsi da amfani da sakamakon fasahar zanani ta AI da kuma hotunan kafafen sada zumunta a matsayin hujja kamar yadda daraktan sashen fasahar sadarwar zamani na hukumar Lawrence Bayode ya bayyana.
A bayanin da ya yi a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels ya ce hukumar ba za ta dogara da hujjojin da ba su da tabbas ba wajen tantance gaskiyar lamarin.
Bayode ya jaddada cewa hukumar zaɓe za ta dogara ne kacokan kan hujjojin da ke da tabbas da kuma binciken ƙwararru domin tabbatar da ko asusun yana da alaƙa da shugaban hukumar ko kuma abin da ake yaɗawa na gaskiya ne.
Hayagagar taƙaddamar dai na nuna irin girman ƙalubalen da dimokuraɗiyyar Nijeriya ke fuskanta yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 domin kuwa jam’iyyar ADC da magoya bayanta na ganin wannan yunƙuri ne na kare sahihancin zaɓe a yayin da hukumar zaɓe ke ganin matsin lambar yunƙuri ne kawai na siyasa da ke iya kawo cikas ga ƴancin gudanar da ayyukan ta.
Tuni dai sake ɓullar saƙon Ɗ da aka alaƙanta da asusun shugaban hukumar zaɓe ya harzuƙa al’umma da suka fara yekuwar kiran ya sauka daga muƙaminsa wanda a dalilin hakan a kafafen sada zumunta suka ƙirƙiri alamar wajibi ne Amupitan ya sauka kan rashin alƙibla ɗaya a zaɓen 2027.
A cewarsu saƙonnin nuna goyon bayan APC da Shugaba Tiinubu da ya wallafa a baya sun nuna a fili rashin amanna da sahihancin hukumar a ƙarƙashin jagorancinsa ga aiwatar da zaɓen gaskiya da gaskiya a 2027
Wakilin mu ya labarto cewar tuni al’ummar ƙasa suka bayyana cewar idan har shugaban hukumar ya damu da kima da martabar hukumar to ya sauka daga muƙaminsa ba tare da kai ruwa rana ba.
Tun da farko dai ƙungiyar Musulmai ta Muslim Rights Concern (MURIC) ta fito fili ta yi kiran da a cire shugaban hukumar zaɓe daga kujerarsa a bisa ga kokonton gudanar da sahihin zaɓe bisa kalamansa na ƙin jinin Musulunci da Musumai.
Haka ma majalisar ƙoli ta shari’a a Nijeriya ta bayyana damuwa kan rashin tsayuwa tsakiya a zaɓen 2027 tare da cewar kaucewa ga yin hakan zai shafi yadda da amincin hukumar wajen gudanar da zaɓe nagari.
Majalisar ta bayyana cewar mutumin da ya nuna ƙin jinin Musulunci ba zai gudanar da adalci a zaɓen da zai jagoranta ba don haka abu ne mawuyaci al’ummar Musulmi su karɓi sakamakon zaɓen da zai gudanar wanda a kan hakan ne suka buƙaci ya sauƙawawa kansa ya sauka daga shugabancin hukumar.
Haka ma ƙungiyoyin farar hula da dama a Nijeriya sun bayyana damuwarsu kan sahihancin zaɓe a ƙarƙashin Farfesa Amupitan wanda a kan hakan suka buƙaci murabus ɗin sa domin bayar da ƙofar gudanar da zaɓen da dukkanin al’umma za su aminta.
Ƙungiyar ActionAid Nijeriya na cikin ire- iren ƙungiyoyin a inda ta bayyana cewar zarge-zargen nuna son kai na iya lalata amincewar jama’a ga sahihancin zaɓen 2027 wanda al’umma ke son fafatawa domin zaɓen shugabannin da suke muradi.
Daraktan ƙungiyar a Nijeriya, Andrew Mamedu ya ce ko da zargin ya samo asali ne daga tsoffin ra’ayoyi, har yanzu yana iya jefa shakku kan rashin nuna wariyar shugabanci don haka murabus ɗin sa zai taimaka wajen dawo da martabar hukumar zaɓen ga al’ummar da suka dawo daga rakiyar ta.
Shugaba Tiinubu ya naɗa Farfesa Joas Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓe a watan Oktoba 2025 bayan kammala wa’adin Farfesa Mahmus Yakubu.
Bayan rantsar da shi, shugaba hukumar ya yi alƙawarin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da sahihanci tare da kare ƴancin kai da mutuncin hukumar zaɓe ta ƙasa, lamarin da a yau jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar da al’ummar ƙasa da dama ke tababar gudanar da sahihin zaɓe a ƙarƙashin jagorancin sa.















Discussion about this post