ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Rashin Hadin Kan ‘Yan Adawa Ya Ba Tinubu Tazarce A Cikin Sauki —Ahmad Zangina

by Sulaiman
4 months ago
zangina

Ahamad Sani Zangina matashin dan siyasa ne kuma mai fafutukar kare hakkin al’umma. Yana kuma daga cikin wadanda suka amince da tafiyar jagorancin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. A tattaunawarsa da Editanmu Bello Hamza a ofishinsa da ke Abuja, ya bayyana yadda rikici da kwadayin mulki na ‘yan adawa zai tallafa wa Shugaba Tinubu yin tazarce a cikin sauki. Ga dai yadda hirar ta kasance.:

Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka.

Da farko dai sunana Ahmad Sani Zangina, dan Nijeriya mai yi wa kasa fatan Alhairi

ADVERTISEMENT

A yayin da sararin siyasar Nijeriya ta turnuke, ya kake ganin yiyuwar samun nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2027.

Wato yadda ‘yan adawa suke tafiyar da harkokin kalubalantar gwamnatin Tinubu tamkar suna kara bashi damar lashe zabe ne ta hanyar yin tazarce a cikin sauki, saboda jam’iyyun adawar sun kasa daidaita kansu saboda kwadayin Mulki ya mamaye zukatansu ba wai kishin kasa ko talakawa suke yi ba. Haka ya hana su kafa jam’iyya daya dilo da za su yi adawa a ciki, saboda haka wannan dambarwar da suke yi yana bai wa Shugaba Tinubu damar yin tazarce kai tsaye ba tare da wata matsala ba, hakan kuma yana yi mana dadi.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gangamin ‘yan adawar baya baku tsoro?

Lallai babu wani dan jam‘iyyar APC ko wani masaoyin Tinubu da wannan taron ‘yan adawar zai  bashi tsoro, musamman ganin yadda manyan ‘yan adawar kamar su Obi da Kwankwaso suka ware daga tafiyar ‘yan adawa, hatta ‘ya’yan shugaban ‘yan adawar Atiku Abubakar da yawa duk sun koma wajen tafiyar Shugaba Tinubu, ashe kaga ya kamata dukkanmu muna mu kwashe inamu inamu mu koma wajen Tinubu don ganin ya samu nasara a zaben da ke tafe domin ci gaban kasar mu Nijeriya.

Ko akwai wasu ayyuka masu muhimmanci da za su saTalaka ya ji ya kamata ya sake zabar Tinubu?

Cikin manyan nasarorin da shugaban Tinubu ya samu a cikin shekarun da ya yi yana mulkin Nijeriya su ne yadda ya samar mana da tsaro a manyan hanyoyi da garuruwan kasar nan musamman a yankin arewacin Nijeriya. idan zan iya tunawa daya daga cikin dalilan da suka sa na ki zabar jam’iyyar APC a lokacin Marigayi Shugaba Buhari shi ne yadda matsalar tsaro ta ta’azzara, musamman kuma ganin yadda yawancin ‘yan arewa ne suke rike da mukaman da suka shafi bangaren tsaro. Tafiye-tafiye cikin kasa ya gagara saboda matsalar tsaro amma cikin ikon Allah tun daga hawan Shugaba Tinubu yanzu zaka iya tafiya daga Kaduna zuwa Abuja da wasu sassan kasar nan ba tare wani tsoro ko fargaba ba. Saboda a halin yanzu an samu sauki sosai. Lallai ya yi kokari sosai. A bangaren tattalin arzikiki kuma, lallai Shugaba Tinubu ya yi kokari sosasi, musamman a bangren abinci, farashin shinkafa da masara da sauransu sun yi tashin gwauron zabbi musamman a lokacin da aka janye tallafin man fetur amma cikin hikimar Tinubu a yanzu al’umma suna sayen abinci ba tare da takura ba. Wannan na daga cikin dalilan da zai sa ‘yan Nijeriya su rungumim tafiyar Tijnubu ba tare da wani matsala ba.

Wane irin gyara kake ganin ya kamata Tinubu ya yi kafin zaben 2027, wadanda za su karfafa samun nasararsa?

Gyaran da ta kamata Tijnubu ya yi a gabannin zaben 2027, ya riga ya yi su, kasancewar shi mutum ne mai son ci gaban kasa, tuni ya tabbatar da jihohi suna samun kudaden da ba a taba samun gwamnatin da ta ba jihohi ba. Ya kuma yi tsaye wajen ganin jihohin suna amfani da kudaden ne wajen gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa rayuwar talaka. Ya kuma tsayu wajen ganin ‘ya’yen talakawa sun samu ingantaccen ilimi a dukkan matakai musamman a manyan makarantun kasar nan, a kan haka ya kirkiro da tsarin ba ‘yan makarantun jami’a tallafin karatu da kudaden da za su sa a aljihu domin gudanar da karatunsu cikin natsuwa (NELFUND). Tabbas wadannna suna daga cikin manyan ayyukan da Tinubu ya yi da za su talaka ya zabe shi a 2027.

Zuwa yanzu an fara samun tayar da jijiyar wuya a wash jihohi sakamakon zaben fidda da gwamni na ‘yan takara, menene shawarar ka ga ‘yan siyasa?

Kira na ga ‘yan siyasa da suka fara tayar da jijiyan wuya sakamakon rashin nasara a zabukkan fidda ga gwani na jam’iyyar APC, musamman kamar irin su Farfesa Isa Pantami. Ya kamata su sani cewa, babu yadda za a yi a ba mutum biyu takarar gwamna a jiha daya, dole a samu wasu su yi hakuri, amma in har ka yi biyayya ka muna cewa kai mai kaunar nasarar jam’iyyar ce, kai ma kana iya samun wani babban rabo a nan gaba, amma in har ka nace da cewa dole sai  kai za a ba kuma ko da kai aka ba sai wasu sun yi gunagunii a kan haka ya kamata kowa ya kai zuciya nesa, ya zama kowa yana kokarin tabbatar da ganin jam’iyya ta yi nasara ne a dukkan matakai. A kan haka ina kira ga dukkan ‘yan jam’iyyarmu su kai zuciya nesa, su kuma bayar da goyon baya ga wanda aka zaba, ta haka za a samu nasarar da ya kamata.

Ko akwai wani jawabi da kake son yi wa ‘yan Nijeriya game da zaben 2027?

Jawabi na karshe ga ‘yan Nijeriya shi ne su kara hakuri tare da ba Shugaba Tinubu dukkan goyon bayan da ake bukata domin samun cikakkiyar nasara ga jam’iyyar APC a dukkan matakai na zabukkan da ke tafe. Tabbas za mu ga canji a harkokin gudanarwa kasar nan. Muna da yakinin Tinubu dan siyasa ne da ba a taba samun kamarsa ba a kasar, domin yana kishin ci gaban Nijeriya. Ya kuma shirya fito da tsare-tsaren da za su bukasda rayuwar al’umma a cikin kankanin lokaci. Allah ya ba mu sa a.

Mun gode sosai

Nima na gode

zangina
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
An Sake Karrama Gwamna Dauda Lawal Da Lambar Yabo Kan Mulki Na Adalci A Zamfara

An Sake Karrama Gwamna Dauda Lawal Da Lambar Yabo Kan Mulki Na Adalci A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.