2027: ’Yansanda Za Su Ba ’Yan Nijeriya Mamaki Da Kyakkyawan Aiki A Lokacin Zaɓe — IGP
Sufeto-Janar na ’Yansandan Nijeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa rundunar ’yansanda za ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa kafin zaɓen 2027, a lokacin zaɓen da kuma bayan kammala zaɓen.
Disu ya ce yadda jami’an ’yansanda za su gudanar da ayyukansu a lokacin zaɓen zai sa ’yan Nijeriya su yi farin ciki da kuma alfahari da rundunar.
IGP ɗin ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Talata a Fatakwal, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ƙaddamar da wani littafi mai taken “The Origin of Women in Nigeria Police Force” (Asalin Matan da Suka Yi Aiki a Rundunar ’Yansandan Nijeriya).
Dame Stella Okuyiga, mai shekaru 96, wadda ta yi ritaya daga mukamin mataimakiyar kwamishinan ’yansanda (DCP), ce ta rubuta littafin. Tana daga cikin mata 20 na farko da suka fara aiki a Rundunar ’Yansandan Nijeriya (NPF).
Da yake magana kan shirye-shiryen rundunar domin zaɓen 2027, Disu ya ce sun gudanar da taro da kwamishinonin ’yansanda na jihohi da sauran manyan jami’ai a faɗin ƙasar.
Ya bayyana cewa manufar taron ita ce nazarin abubuwan da suka faru a zaɓukan baya da kuma ƙarfafa dabarun rundunar wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaɓe.













