Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da shari’ar da Gwamnatin Jihar Kwara ta shigar kan tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, bisa zargin ɓata suna da cin zarafi ta yanar gizo.
Kotun ta yanke hukuncin cewa zarge-zargen da kuma shaidun da aka gabatar ba su nuna cewa Saraki ya aikata wani laifi ba.
A hukuncin da Mai Shari’a Ridwan Maiwada Abdullahi ya zartar, kotun ta ce babu wata shaida da ta nuna cewa kalaman Saraki sun tunzura mutane ko sun haddasa tashin hankali a jihar.
Ta ce shaidun sun nuna ne kawai cewa wasu mutane ba su ji daɗin kalaman nasa ba.
Shari’ar ta samo asali ne daga kalaman Saraki da ya yi zargin cewa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq bai kammala karatun sakandare ba, kuma matakin karatunsa yana shafar yadda yake yanke hukunci.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Saraki ya ce hakan ya ƙara tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya hana mutane bayyana ra’ayoyinsu kan ayyukan gwamnati.
Ya kuma yaba wa ɓangaren shari’a bisa kare gaskiya da tabbatar da adalci.













