ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Yunƙurin Sauya Shettima A Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Ɓaraka Zai Janyo A APC – Matasa

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
8 months ago
APC

Majalisar Matasa ta Jam’iyyar APC wato (APC Youth Parliament) ta yi kakkausar gargaɗi kan jita-jitar da ake ta yaɗawa da ke cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tana bayyana irin waɗannan yunƙurin a matsayin masu hatsari, masu neman janyo rarrabuwar kai, kuma masu iya kawo cikas ga nasarar jam’iyya mai mulki.

Kungiyar ta ce ta lura kuma ta damu kan yadda wasu rahotanni ke ƙara yawo a wasu sassan kafafen yaɗa labarai da ke zargin cewa Shugaba Tinubu na tunanin ajiye Shettima tare da maye gurbinsa da wani Kirista ɗan Arewa, wai domin rage sukar tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi amfani da shi a zaɓen 2023.

ADVERTISEMENT
  • Darajar Tamburan Kasar Sin Sun Karu A Duniya 
  • AFCON 2025: Lookman Da Osimhen Na Daga Cikin Zaratan Yan Wasa 11 Na Bana

Da ya ke magana da ’yan jarida a Bauchi ranar Litinin, Shugaban Majalisar Matasa ta APC, Kabiru Garba Kobi, ya yi watsi da jita-jitar, yana cewa an ƙirƙire ta ne da gangan domin haddasa rikici a cikin jam’iyyar APC.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

A cewar Kobi, waɗanda ke yaɗa irin waɗannan raɗe-raɗin su na yi ne don muradunsu na ƙashin kai, ba wai don neman haɗin kai da daidaiton jam’iyyar ba.

“Duk wani yunƙuri na sauya Sanata Kashim Shettima babban kuskure a siyasance ne da zai iya jawo wa Shugaba Tinubu asarar ƙuri’u mai yawa a Arewa, musamman Arewa-Maso-Gabas,” in ji Kobi.

Ya lura cewa masu yaɗa batun na cewa Shugaba Tinubu na duba yiwuwar zaɓan Kirista ɗaya daga cikin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, Ministan Tsaro Laftanar-Janar Christopher Musa (mai ritaya), Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang, da Limamin Katolika na Sokoto, Rabaran Matthew Hassan Kukah domin sauya Shettima da ɗaya daga cikinsu. Kobi ya ce irin waɗannan hasashe kawai da ruɗani da wasu ‘yan siyasa ke haddasawa.

Kobi ya amince cewa Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya bai wa Shugaban Ƙasa damar zaɓar abokin takararsa daga ko’ina a faɗin ƙasar, amma ya jaddada cewa hikimar siyasa, riƙon amana, aminci, da gaskiya su ne ya kamata su jagoranci irin wannan matakin.

“Duk abin da ake buƙata daga mataimaki, aminci, sadaukarwa, jarumtaka, gogewar siyasa, da goyon bayan jama’a, Sanata Kashim Shettima na da su ba tare da shakka ba,” in ji shi.

Shugaban Majalisar Matasa ta APC ya jaddada cewa Shettima har yanzu shi ne mafi haɗa kan al’umma a Arewa-Maso-Gabas kuma jigo a arewa baki daya da sauran sassan ƙasar nan.

“Shettima shi ne mutumin da zai iya tara Arewa ya kawo ƙuri’un da Shugaba Tinubu ke buƙata a 2027. Waɗanda ke kiran a sauya shi, ba wata gudummawar da suka bayar wajen nasarar APC a 2023. Wasu daga cikinsu ma sun yaƙi Tinubu a wancan lokaci, amma yanzu wai su ke neman a sauya wanda ya bada gudunmawa sosai wajen nasarar Tinubu,” in ji Kobi.

Ya kuma yi gargaɗi ga Shugaba Tinubu da kada ya saurari masu rura wannan yunƙurin, “Muna roƙon Mai Girma Shugaban Ƙasa kada ya bari a shagaltar da shi da waɗanda ba su taɓa kasancewa ɓangare na gwagwarmayarsa ba. Cigaba da tafiya da Shettima shi ne hanya mafi tabbas ta samun nasara a 2027,” in ji shi.

Kobi ya bayyana cewa Majalisar Matasa ta APC ta yi tur da duk wani yunƙuri na janyo cikas ga tikitin Tinubu/Shettima, yana mai cewa ƙarfin jam’iyyar yana tattare da nasara, amincewa, da jagoranci da aka gwada.

Da ya ke bayyana Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima a matsayin shugaba mai hangen nesa, kuma mai kishin ƙasa, Kobi ya ce jajircewarsa da salon jagorancinsa na ci gaba da zaburar da matasan Nijeriya.

Ya kwatanta tasirin siyasar Shettima a Arewa-Maso-Gabas da na Firayim Ministan Nijeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, yana cewa matasan yankin na kallonsa a matsayin alamar jarumtaka, sadaukarwa, da haɗin kan ƙasa.

Shugaban Majalisar Matasa ta APC ya yi gargaɗi cewa canza matsayin Shettima gabanin 2027 ba wai kawai zai raba jam’iyyar ba ne, har ma zai nisanta miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a na Arewa, waɗanda goyon bayansu ke da matuƙar muhimmanci ga nasarar APC a zaɓe.

APC
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
APC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Gina Tsarin Cajin Motoci Masu Amfani Da Lantarki Mafi Girma A Duniya

Sin Ta Gina Tsarin Cajin Motoci Masu Amfani Da Lantarki Mafi Girma A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.