ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Harbe Mai Unguwa Har Lahira A Bauchi

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
2 months ago
Yansanda

Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Clement Anthony, mai shekaru 40 a duniya, bisa zarginsa da hannu a kisan wani mutum mai shekaru 55 da kuma mallakar bindiga ƙirar gida ba bisa ƙa’ida ba a cikin garin Bauchi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. Ya ce wani mazaunin unguwar Ngas da ke cikin ƙaramar hukumar Bauchi ne ya kai labarin faruwar lamarin ga ofishin ‘uansanda ta ‘A’ Division a ranar 19 ga Yuli, 2026.

Sanarwar ta ce mai shigar da ƙorafin ya shaida wa ‘yansanda cewa akwai zargin cewa Clement Anthony, mazaunin Unguwar Ngas, Inkil, Bauchi, ya ɗauki wata bindiga ƙirar gida mai harsashi guda (harbi-ka-noƙe), sannan da gangan ya ɗambara alburushin wa Malam Jacob Bature, mai shekaru 55, wanda shi ne mai unguwar Ngas, yayin wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

Jacob ya samu munanan raunukan harbin bindiga a gefen dama na ƙirjinsa, inda ya faɗi a sume. Daga nan aka garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

SP Nafiu Habib ya ƙara da cewa an ajiye gawar mamacin a ɗakin ajiyar gawa na asibitin domin ci gaba da bincike.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Jami’an ‘yansanda sun yi gaggawar kama wanda ake zargin, tare da ƙwato bindigar ƙirar gida mai harsada ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin, da kuma kwanson harsashi guda da aka harba.

Nafiu ya ce an miƙa kes ɗin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) domin ci gaba da zurfafa bincike. Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah wadai da kisan, tare da jaddada ƙudirin rundunar na tabbatar da cewa duk masu aikata laifuka suna fuskanci hukunci bisa doka.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su guji mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, tare da gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko abu da ake zargi da shi zuwa ofishin ‘yansanda mafi kusa.

Yansanda
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi
Yansanda
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Bayar Da Tallafin Sama Da Ton 3,000 Na Abinci Ga Sudan Ta Kudu

Kasar Sin Ta Bayar Da Tallafin Sama Da Ton 3,000 Na Abinci Ga Sudan Ta Kudu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.