ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

by Yusuf Shuaibu
2 weeks ago
INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta gano barazanar tsaro da tashin hankali a wajen zabe a wasu wurare da sayen kuri’a da kalaman batanci da bayanan karya d katsalandan da rudani na bayanin, a matsayin manyan barazana ga sahihancin zaben 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, shi ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja yayin da yake karbar wata tawagar daga cibiyar kasa da kasa ta duniya (IRI), wadda tsohowar mataimakinyar sakataren harkokin wajen Amurka kan harkokin Afirka, Ambassador Jendayi Frazier ta jagoranta.

Amupitan ya ce barazanar da aka gano na iya rage amincewar masu kada kuri’a kuma su haifar da manyan kalubale ga tsarin zabe idan ba a magance su yadda ya kamata ba.

ADVERTISEMENT

“Hatsarin tsaro, tashin hankali na zabe a wasu yankuna, sayen kuri’a, yaduwar kalaman batanci, bayanan karya, katsalandan da kuma watsa bayanan karya daga kasashen waje suna kawo barazana kai tsaye ga amincewar masu kada kuri’a,” in ji shi.

Shugaban INEC ya ce aikin tantancewar ya bayar da hangen nesa na ‘yanci yayin da hukumar ke canjawa zuwa cikakken shirye-shirye don tunkarar zaben 2027.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Ya bayyana cewa INEC na kara karfin ayyukanta don tura kusan ma’aikata na wucin gadi miliyan 1.4 a fiye da rumfunan zabe 176,000 a duk fadin kasar yayin zaben 2027.

Amupitan ya kuma ce hukumar na amfani da tsarin tantance hoto da na’urar ABIS, don kawar da bayanai masu maimaituwa da tabbatar da rajistar masu zabe.

A cewarsa, zaben gwamnan da zaben cike gibi na ‘yan majalisa da aka yi kwanan nan ba kamar zaben gama-gari ba ne, wadannan zabuka sun kasance kamar gwaje-gwaje na aikin hukumar wajen samar da dabarun aiki, tsaro da tsarin fasaha.

Ya ce amfani da fasaha ya rage matsaloli da ke tattare da tsarin kada kuri’un Nijeriya fiye da na baya.

“Kwazon tsarin aikin tantance masu zabe ta na’urar BBAS, don tabbatar da bayanan mutum da kuma bayyana sakamakon zabe a shafin INEC da na’urar IReB suna ci gaba da nuna babban dogaro wajen aiki, suna samun adadin lodawa sama da kashi 98 cikin dari a zaben da aka gudanar a baya,” in ji shi.

Amupitan ya ce taswirar aiki ta hukumar ta hada da binciken rajistar masu kada kuri’a, shirye-shiryen tura ma’aikata da kungiyoyin sufuri tun da wuri don tabbatar da cewa an bude ramfan kada kuri’a kafin karfe 8:30 na safe, da kuma inganta kayan taimako ga masu nakasa da mata masu juna biyu da tsofaffin masu kada kuri’a.

Game da barazanar tsaro da kudi kuwa, ya ce INEC na aiki tare da jami’an tsaro a karkashin kwamitin tattaunawa na hukumomin tsaro kan zabe (ICCES), da kuma hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, ciki har da hukumar kula da laifukan tattalin arziki da kudade (EFCC) da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Ya ce hadin gwiwar na nufin aiwatar da dokokin kudi na yakin neman zabe da sa ido kan laifukan zabe da tabbatar da an gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa hukumar za ta hadu da ‘yan takarar shugaban kasa daga don sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kwamitin zaman lafiya ta kasa kan matsaolin yakin neman zabe, wanda aka gudanarwa don inganta ladabi tsakanin masu harkokin siyasa.

Ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta sauya tsarin ta ba, Amupitan ya tabbatar wa tawagar kasa da kasa cewa INEC za ta yi gaskiya kuma za ta hadi kai a duk tsawon aikin zabe.

“A matsayinmu na hukumar gudanar da zabe, babban aikinmu shi ne mu zama alkalin da ba ya karkata ga kowa, wanda ke yin aiki ba tare da son rai ba don samar da zaben da ya kasance mai cike da adalci, wanda ya bi tsarin doka, kuma wanda ke nuna sahihin ra’ayin ‘yan Nijeriya,” in ji shi.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: Ƴan Nijeriya Za Su Kori APC Idan Har An Gudanar Da Sahihin Zaɓe – Shugaban PRP

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Tambarin Dimokuradiyya

2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

August 28, 2026
Next Post
Adadin Masu Amfani Da Wayar Salula Mai Tsarin Sadarwar 5G A Kasar Sin Ya Wuce Kashi 70%

Adadin Masu Amfani Da Wayar Salula Mai Tsarin Sadarwar 5G A Kasar Sin Ya Wuce Kashi 70%

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.