Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ƴan Nijeriya za su kori jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2027, muddin idan aka gudanar da sahihin zaɓe yam ai cike da adalci.
Baba-Ahmed ya yi iƙirarin cewa babban abin da ya kamata APC ta damu da shi ba jam’iyyun siyasa na adawa ba, amma ta damu da ƴan Nijeriya masu kaɗa kuri’a, waɗanda su ne za su yanke hukunci na ƙasarshe a zaɓen 2027.
Ya yi waɗannan sharhi ne yayin da yake tattaunawa kan sake tsara haɗin gwiwar siyasa da dabarun adawa kafin zaɓukan shekarar 2027 a wani shiri na gidan talabijin Alheri a Jihar Kaduna.
A cewarsa, jam’iyyun siyasa ba su yanke sakamakon zaɓe, masu jefa ƙuri’a su ne ke yanke wane ƴan takara da jam’iyyun za su yi nasara.
“Suna sane cewa idan suka bari aka gudanar da sahihin zaɓe mai cike da gaskiya, ƴan Nijeriya ba za su kaɗa ƙuri’a a gare su ba. Wannan shi ne abin da suke tsoron,” in ji shi.
Shugaban PRP ya ƙara da cewa, “Ba saboda hamayya daga wasu jam’iyyun siyasa suke kamata su ji tsoro ba, sai dai hamayya daga ƴan Nijeriya, domin jam’iyyun siyasa ba sa kaɗa ƙuri’a, ƴan Nijeriya ne suke kaɗa ƙuri’a.”
Ya ce APC ta san cewa bari ƴan ƙasa su zaɓi shugabanninsu cikin ƴanci zai iya zama abin da zai sa jam’iyyar ta yi rashin nasara a 2027.
Baba-Ahmed ya kuma gargaɗi ƴan adawa game da sake ƙirƙiro haɗin kai don fatattakar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba tare da samun shiri mai kyau da ba.
“Mun sani akwai wasu mutane da kawai suke neman a cire Tinubu domin su yi abin da suke so, ko su maimaita irin manufofin da Tinubu yake aiwatarwa a yanzu. Daga baya, watakila su ce an samu kuskure,” ya yi gargaɗi.
Ya jaddada cewa PRP ba zai goyi bayan wani ɗan siyasa ba kawai bisa ga burinsa na zama shugaban ƙasa.
“A PRP, ba za mu yarda mu goyi bayan wani kawai saboda yana da burin zama shugaban ƙasa ba. Ba za mu shiga irin wannan tsari ba. Dole mu fara ganin abin da suke niyya kafin mu yarda da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa kowace haɗin gwiwar siyasa da PRP ta goyi baya dole ne ta sami tsare-tsare bayyananne na magance manyan matsalolin Nijeriya, kamar rashin tsaro, talauci, yunwa, da rashin jin daɗin jama’a gaba ɗaya.
Baba-Ahmed ya lura cewa jam’iyyar za ta duba haɗin gwiwar siyasa da ke tasowa kafin shekarar 2027 domin tantance ko sun samo asali ne daga ainihin niyyoyi ko son zuciyar siyasa ta ƙashin kai.
“Za mu iya gane yaudara, kuma za mu iya gane kyakkyawan nufi,” in ji shi.
Ya ce a shirye jam’iyyarsa take domin yin haɗakar da zai kayar da Tinubu a zaɓen 2027, idan ƴan adawa sun haɗa kai a tsakaninsu kafin zaɓen.














