ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027:Kwamishinoni 6 Sun Yi Murabus A Jihar Bauchi

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Bala Mohammed

Babban Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Hon. Aminu Hassan Gamawa, tare da kwamishinoni shida sun yi murabus daga Majalisar Zartarwa ta Jihar (SEC) domin neman cikar burin siyasa gabanin zaben 2027.

Wadanda suka yi murabus sun hada da Yakubu Adamu (Ma’aikatar Kudi da Ci gaban Tattalin Arziki), Abdurrazak Nuhu Zaki (Ma’aikatar Albarkatun Ruwa), Hajara Yakubu Wanka (Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Agajin Gaggawa), Isa Babayo Tilde (Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu), Hon. Faruk Mustapha (Ma’aikatar Ci gaban Karkara da Ayyuka na Musamman), da sauransu.

Bayan murabus din, Gwamna Bala Mohammed ya amince da sauye-sauye cikin gaggawa tare da bai wa wasu mambobin majalisar zartarwa alhakin kula da ma’aikatun da abin ya shafa har sai an nada sabbin kwamishinoni.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar jiya, an umarci Hashimu Yakubu, Babban Sakataren Sirri na Musamman (PPS), da ya kula da ofishin Babban Sakataren Gwamnati.

Gwamnan ya kuma tura tsohon kwamishinan ilimi, Dakta Mohammed Lawal Rimin Zayam, a matsayin kwamishina na Ma’aikatar Wutar Lantarki, Kimiyya da Fasaha.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Haka kuma, Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Hassan Usman El-Yakub (SAN), zai kula da Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, yayin da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, Usman Usman Shehu, zai jagoranci kula da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.

Hakazalika, Kwamishinan Gidaje da Muhalli, Hon. Danlami Ahmed Kawule, an ba shi alhakin kula da Ma’aikatar Ci gaban Karkara da Ayyuka na Musamman, yayin da Amina Muhammad Katagum, Kwamishinar Kasafin Kudi, Tsare-tsare da Hadin Gwiwa na Kasashe, za ta kula da Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Agajin Gaggawa.

Bugu da kari, Mohammed Sadik Shira, Kwamishinan Harkokin Kungiyoyi da Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs), zai kula da Ma’aikatar Kudi da Ci gaban Tattalin Arziki, yayin da tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yansanda (DIG mai ritaya) Sani Mohammed, mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro, zai kula da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Jama’a.

Yayin da yake yi wa wadanda suka yi murabus fatan alheri a sabbin matakan da za su shiga, Gwamna Bala Mohammed ya bukaci wadanda aka sake tura su da su dauki cikakken alhakin ayyukansu tare da amfani da kwarewarsu wajen tafiyar da ma’aikatun.

Ya kuma umarce su da su yi aiki tare da manyan sakatarorin ma’aikatun domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.

Bauchi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Bauchi
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada

An Yi Kira Da A Kara Tallafi Kan Lamarin Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.