ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 6, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Halascin Yanke Farce Ko Aski Ga Wanda Ya Yi Niyyar Layya

by Najibullah Mohammed
2 years ago
Layya

Yin aski ko yanke farce a goman farko na Zulhijja ba ya hana yin layya ko idan an yi ta zama karbabbiya ko ingantacciya, muddin mai layya ya cika sharuddan da shari’a ta ajiye a kan yin layyarsa, akwai sharudda a kan kansa, akwai sharudda akan layyarsa, akwai kuma sharudda akan dabbar.

Sharudda a kansa ya zama yana da iko na yin layyar, yanka kuma wajibi ne a yi ranar sallah bayan limamin da yake masu salla a garinsu ko a unguwarsu ya yanka dabbarsa, ko kuma ya bada izini kowa ya yanka layyarsa,duk wanda ya yanka dabbarsa kafin liman ya yanka tashi yankansa bai yiwu ba, ita kuma dabbar da za a yanka lallai ne ta zama daga cikin dabbobin ni’ima, wato Rakuma, Shanu, Tumakai da Awakai, kuma lallai ne dabbar ta zama ta cika shekarun girma jinsinta, kuma ba ta da nakasa ko wata illa kamar makanta ko gurguntaka ko rauni wanda yake fitar da jini bai warke ba.Muddin an cika wa’dannan sharuddan aka yi yankan nan to layya ta yi. Yin askin mai layya ko yanke farcensa bai shafi ingantuwar layyarsa ba ko rashin ingantuwarta.

  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Tsarin Kamfanoni Na Zamani Mai Halayyar Musamman Ta Sin
  • Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 4

Da yawa mutane su na daukar hadisin uwar Muminai Nana Ummu Salama wacce ta rawaito cewa; Annabi (SAW) ya ce, idan watan Zulhijja ya kama duk wanda yake da abin yanka wanda zai yanka a matsayin layya to kada ya yi aski ko yanke farce a wadannan kwanuka har sai ya yi layyarsa. Wannan hadisi an ganshi a cikin littafin Imamu Muslim.

ADVERTISEMENT

Abinda muke jan hankalin mutane a kansa, litattafan hadisai musamman su manyan litattafai wato irinsu Bukhari da Muslim da sauransu abin da suka shardanta wa kansu cewa za su kawo dukkan hadisan da suka inganta cewa Annabi (SAW) ya fade su, amma ba su dora wa kansu ba yi wa mutane bayanin cewa wannan hadisi har yanzu yana aiki ko ba ya aiki, ko wannan hadisi akwai wani hadisin da ya dakatar da aikinsa ko ya rage fadin aikinsa ko ya kara fadin aikinsa, su dai kawai su na kawo hadisai ne ingantattu daga Annabi (SAW). Ba za ka iya gane cewa wannan hadisi har yanzu yana aiki ko ba ya aiki ba ko mene ne fadin ma’anarsa, ko me ake nufi da shi sai ka koma wajen malamai masana su ne za su yi ma wannan bayanin.

Kamar yadda a Alkur’ani za ka iya samun ayoyi tuli wadanda ga su nan har yanzu Alkur’ani ne ana karanta su amma kuma aiki da su an dakatar da shi. Bari mu ba da misalin guda daya. Fadin Allah (SWT) da yake cewa; Sura: 2 aya: 234, “Duk wadanda suka mutu daga cikinku suka bar matansu, matan za su zauna har tsawon wata hudu da kwana goma kafin su yi aure (wato zaman takaba ke nan).”

LABARAI MASU NASABA

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

Sai ga wata aya ita kuma a cikin dai wannan sura: 2, aya: 240; Allah yana cewa; “Wadanda suka mutu daga cikinku suka bar mata ana ba matansu umarni zama tsawon shekara guda ba tare da fita ba kafin su yi aure.”

Dukkan wadannan ayoyi guda biyu ayoyi ne na Alkur’ani kuma har gobe ana karanta su,amma daya ta warware hukuncin daya, saboda haka dole ne daya za a dauka daga ciki, ba za a yi amfani da dayar ba.

Irin wadannan misalai suna da yawa a cikin Alkur’ani da hadisan Annabi (SAW). Shi ya sa wannan hadisi da muka fada a sama na uwar Muminai Ummu Salama Allah ya yarda da ita, hadisin Nana A’isha uwar Muminai Allah ya yarda da ita ya warware shi, inda take cewa;

Ita ce take shirya dabaibayi da igiyar daure dabbobin da Manzon Allah (SAW) zai yi layya da su ya aika su zuwa Harami, idan ya yi haka Annabi (SAW) bai taba hana kansa wani abu da Allah ya halatta mashi ba saboda dalilin ya yi niyyar zai yi layya. Shi ma dai wannan hadisi Imamu Muslim ne har yau ya rawaito shi, ta yadda za ka gane cewa Imamu Muslim yana kawo hadisai ne da suka inganta daga Annabi (SAW) ba yana aikin cewa wannan ana aiki da shi ko wannan ba a aiki da shi ba, kamar yadda aka rawaito hadisin da Annabi (SAW) aka tambaye shi a kan hukuncin wanda ya shafi azzakarinsa bayan ya yi alwala, Annabi (SAW) ya ba da amsar cewa azzakari wani bangare ne na jikin mutum saboda haka don mutum ya shafe shi alwalarsa tana nan, sai kuma ga wani hadisi shi kuma Annabi (SAW) yana cewa; Duk wanda ya shafi azzakarinsa bayan ya yi alwala to ya sake yin alwala.

Su ma wadannan hadisai guda biyu dukkansu Imamu Hajar Al-Askalani ya kawo su a cikin Albulugul Maram.

Saboda haka muke jan hankalin mutane da cewa yin aski ko yanke farce bai shafi hukuncin layya ba, ingancinta ko rashin ingancinta ba, suna nan a kan hukuncinsu. Akwai wasu malamai wadanda suke nuna cewa yin aski ko yanke farce dama ce ta mutum idan yana so ya yi idan kuma ba ya so sai ya bar shi, saboda ganin cewa idan an zo lissafa ladan da zai samu idan ya yi layya za a lissafa dukkan kwayar gashi da ta ke jikinsa, to idan ya aske su wai ba za a lissafa da su ba. To amma shi gashi ranar da aka aske shi washegari ma fitowa yake yi kuma wannan ba zai sa a ki lissafawa da shi ba.

Allah ya sa mu dace, amin.

Layya
Najibullah Mohammed
+ postsBio

    MASU ALAKA

    Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
    Siyasa

    Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

    May 5, 2026
    MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi
    Addini

    MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

    May 2, 2026
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
    Addini

    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

    March 20, 2026
    Next Post
    Jiragen Dakon Kaya Masu Zirga-zirga Tsakanin Sin Da Turai Sun Gudanar Da Zirga-zirga Mafi Yawa A Mayu

    Jiragen Dakon Kaya Masu Zirga-zirga Tsakanin Sin Da Turai Sun Gudanar Da Zirga-zirga Mafi Yawa A Mayu

    LABARAI MASU NASABA

    Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai A Yankin Arewa Maso Gabashin Sin Ya Zarce 3,000 A Bana

    Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai A Yankin Arewa Maso Gabashin Sin Ya Zarce 3,000 A Bana

    June 6, 2026
    Kofin Duniya: Sababbin Dokokin Da FIFA Ta Kawo

    Kofin Duniya: Sababbin Dokokin Da FIFA Ta Kawo

    June 6, 2026
    Kafar CMG Ta Kulla Yerjeniyoyin Hadin Gwiwa Da Hukumomin Kasar Laos

    Kafar CMG Ta Kulla Yerjeniyoyin Hadin Gwiwa Da Hukumomin Kasar Laos

    June 6, 2026
    Rundunar Sojan Kasar Sin Ta Sa Ido Kan Jirgin Ruwan Yakin Kasar Holland Da Ya Tsallake Mashigin Tekun Taiwan

    Rundunar Sojan Kasar Sin Ta Sa Ido Kan Jirgin Ruwan Yakin Kasar Holland Da Ya Tsallake Mashigin Tekun Taiwan

    June 6, 2026
    Sin Tana Adawa Da Karin Takunkumin Da Amurka Ta Sanya Wa Cuba

    Sin Tana Adawa Da Karin Takunkumin Da Amurka Ta Sanya Wa Cuba

    June 6, 2026
    Matsalar Tsaro Da Tsadar Kayan Noma Na Barazana Ga Samar Da Abinci A Daminar Bana

    Matsalar Tsaro Da Tsadar Kayan Noma Na Barazana Ga Samar Da Abinci A Daminar Bana

    June 6, 2026
    Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

    Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

    June 6, 2026
    Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

    Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

    June 6, 2026
    Darajar Naira Ta Sauka A Kasuwar Musayar Kuɗaɗe

    Darajar Naira Ta Sauka A Kasuwar Musayar Kuɗaɗe

    June 6, 2026
    Yadda Ake Miyar Margi Da Kifin Tarwad

    Yadda Ake Miyar Margi Da Kifin Tarwad

    June 6, 2026

    © 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

    No Result
    View All Result
    • Gida
    • Labarai
      • Manyan Labarai
      • Kananan Labarai
      • Masarautu
      • Bakon Marubuci
      • Dausayin Musulunci
      • Daga Kasar Sin
      • Nishadi
      • Noma Da Kiwo
      • Sana’a Sa’a
      • Tambarin Dimokuradiyya
      • Taskira
      • Daga Birnin Sin
      • Ado Da Kwalliya
    • Siyasa
    • Wasanni
    • Al’adu
    • Al’ajabi
    • Labaran Kasuwanci
    • Karanta cikin Turanci

    © 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.