Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara sayar da hannun jarin kamfanin ga jama’a, wanda zai bai wa ’yan Nijeriya damar zama masu hannun jari a matatar.
Kamfanin yana sayar da hannun jari biliyan 4.1 kan Naira 525, wanda zai iya samar da kusan Naira tiriliyan 2.15 idan aka sayar da dukkanin hannun jarin.
Ana sa ran za a fara sayar da hannun jarin ne daga ranar 14 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Oktoba, 2026.
Duk ɗan Nijeriya zai iya sayen aƙalla hannun jari 10, wanda zai kashe aƙalla Naira 5,250.
Masu son sayen hannun jarin za su buƙaci yin amfani da dillalin hannun jari mai rijista ko wata kafar saka hannun jari da aka amince da ita.
Za a yi amfani da kuɗaɗen da aka samu wajen faɗaɗa matatar daga ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.4 na ɗanyen mai a kowace rana.
Aliko Dangote ya ce an tsara sayar da hannun jarin ne domin bai wa talakawa da sauran ’yan Nijeriya, ciki har da ’yan kasuwa da direbobi, damar zama masu mallakar wani kaso na matatar.
Kamfanin ya kuma shirya biyan masu hannun jarin riba cikin dala, tare da amfani da kuɗaɗen da yake samu wajen fitar da man fetur da sinadarai zuwa ƙasashen waje.
Sai dai an gargadi masu zuba jari da su yi taka-tsantsan.
Masana sun ce akwai yiwuwar ba za a bai wa masu neman hannun jarin adadin da suka nema ba.
Haka kuma, matsalar samun isasshen ɗanyen mai na iya shafar yawan aikin matatar da kuma ribar da za a raba wa masu hannun jari.














