Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya hana jami’an tsaro kama mutane cikin dare a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin ganawa da sarakunan gargajiya a gidan gwamnatin jihar da ke Lokoja.
Ya ce jami’an tsaro ba su da damar shiga gidajen mutane da daddare domin kama su.
Ododo ya ce idan ana zargin wani da aikata laifi, ya kamata a gayyace shi da rana tare da bin tsarin doka.
Ya buƙaci sarakunan gargajiya su kai rahoton duk jami’in tsaro da ya ƙi bin wannan umarni, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta amince da cin zarafin ’yan ƙasa ba.
Gwamnan ya kuma gargaɗi mutanen da ke taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar ba su abinci, bayanai ko wasu kayan tallafi.
Ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa masu aikata laifuka zai fuskanci hukunci.
Ododo ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan tallafin da yake bai wa Kogi wajen ayyukan more rayuwa da tsaro.
Ya kuma roƙi sarakunan gargajiya su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya gabanin zaɓen 2027.
Gwamnan ya yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji tashin hankali, su mayar da hankali kan manufofi maimakon addini ko ƙabilanci.














