ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sanata Shehu Sani Ya Nemi Gwamnonin Arewa Su Tallafa Wa Bikin Al’adu Na ABU Zariya

by Idris Umar and Sani Bello
3 weeks ago
Arewa

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya yi kira ga jihohin Arewa da gwamnatin tarayya da su tallafa tare da samar da kuɗaɗen gudanar da bikin al’adun Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), yana mai bayyana bikin a matsayin wata muhimmiyar kafa ta inganta al’adu, yawon buɗe ido da kuma ƙarfafa martabar ƙasa.

Shehu Sani ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin bikin Durbar na shekara-shekara na ABUSRC da aka gudanar ranar Asabar, a matsayin wani ɓangare na bikin al’adun ABUSRC na shekara-shekara.

Baƙon na musamman ya yaba wa masu shirya bikin bisa yadda suka shirya gagarumin bikin mai kayatarwa, musamman yadda ɗalibai suka yi ƙoƙarin ingantawa tare da kiyaye al’adu da aƙidojin gargajiya na Nijeriya.

ADVERTISEMENT

“Mun zo nan ne domin shaida bikin al’adu na majalisar Daluban ABU na shekarar 2026, wanda biki ne mai matuƙar kayatarwa. Ina matuƙar alfahari da burgewa ganin yadda matasanmu ke yin duk abin da za su iya wajen ingantawa da kare al’adunmu da kuma tsarin rayuwarmu na gargajiya,” in ji shi.

A cewarsa, al’ada ita ce ke wakiltar asali da ruhin al’umma, yana mai cewa abubuwan da aka nuna na al’adun gargajiya a wajen bikin sun burge shi matuƙa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya kuma bayyana bikin a matsayin wani muhimmin ɓangare na bunƙasa harkokin yawon buɗe ido a Jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya, inda ya buƙaci gwamnatoci su fahimci muhimmancinsa fiye da kasancewarsa kawai wani taron jami’a.

Shehu Sani ya kuma yaba wa masu shirya bikin bisa ƙoƙarinsu, inda ya ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da gudanar da bikin tare da ƙara sabbin abubuwa masu ƙayatarwa da fasahohin zamani a kowace shekara.

An fara bikin al’adun ABUSRC na shekara-shekara ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, ƙarƙashin taken “Unity in Diɓersity: Celebrating Our Heritage, Strengthening Our Future”, wato “Haɗin Kanmu Cikin Bambance-Bambance: Murnar Gadonmu da Ƙarfafa Makomarmu.”

Bikin na kwanaki huɗu ya ƙunshi shirye-shiryen al’adu daban-daban, ciki har da gasar girki da ɗalibai daga jihohi da ƙabilu daban-daban ke wakilta.

Taron ya haɗa ɗaliban jami’ar, ma’aikata da baƙi domin nuna ɗimbin al’adu da tarihi na Nijeriya. An yi taron lafiya, an tashi lafiya.

Arewa
Idris Umar
+ posts Bio
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Yadda Dakta A’isha Mustapha Ta Zama Shugabar Ƙungiyar Likitocin Jihar Kaduna
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Kafafen Sadarwa Na Zamani Wuri Ne Na Bunƙasa Tattalin Arziƙi — Ubale Kiru
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Kungiyar Daliban Jami’ar ABU Ta Gudanar Gasar Girke-girken Abincin Gargajiya A Bude Bikin Al’adu Na Bana
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
Arewa
Sani Bello
+ posts Bio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Arewa

Tinubu Ya Naɗa Yari A Matsayin Darakta-Janar Na Yaƙin Neman Zaɓen 2027

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.