ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Dakta A’isha Mustapha Ta Zama Shugabar Ƙungiyar Likitocin Jihar Kaduna

by Idris Umar
2 months ago
Mustapha

An zaɓi Dakta A’isha Mustapha a matsayin sabuwar Shugabar Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA), reshen Jihar Kaduna, bayan zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata.

Dakta A’isha ƙwararriyar likita ce a fannin mata da haihuwa, wadda ta yi fice wajen ƙwazo, nagarta da hidima ga harkokin kiwon lafiya. Kafin wannan sabon muƙami, ta samu lambobin yabo da dama, ciki har da karramawa daga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a wajen ƙaddamar da shirin PECCIN Launch 2025. 

Haka kuma ta samu ‘Certificate of Eɗcellence in Peer Reɓiewing. daga Global Academy Publisher a shekarar 2024 da kuma Impact Award 2023 daga Oɓarian Cancer Coalition (Eɓery Woman Study).

ADVERTISEMENT

A fannin ilimi ma Dakta A’isha ta samu nasarori da dama, ciki har da zama mafi ƙwarewa a cikin ɗalibi a jarabawar WACS Part I ta fannin Obstetrics and Gynaecology a shekarar 2015, sannan ta lashe kyautar Mafi Kyawun Malama daga ɗaliban likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello a shekarun 2016 da2017.

Ta kuma kasance mafi kyawun ɗalibar da ta kammala karatu a fannin ‘Obstetrics and Gynaecology’ a ABU Zariya a shekarar 2008, tare da zama ‘Oɓerall Best Student’ a jarrabawar NECO daga Federal Goɓernment College Kano

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sabuwar shugabar ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da za ta mayar da hankali a kai akwai kare haƙƙin likitoci, tabbatar da cikakken aiwatar da tsarin albashi da alawus-alawus na CONMESS, inganta walwalar likitoci, samar da tallafin lafiyar ƙwaƙwalwa, inganta inshorar lafiya, tabbatar da ingantattun lokutan aiki, ba da kariyar shari’a ga likitoci da kuma samar da ƙarin damar horaswa da ci gaban ƙwarewa.

A hirar da ta yi da wakilinmu, Dakta A’isha ta ce ta fito takara ne domin yin hidima ga likitoci da kuma tabbatar da adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba. 

Ta bayyana cewa ita ƴar asalin Jihar Kano ce, ta yi makarantar firamare a Hotoro, sannan ta halarci Federal Goɓernment College Kano kafin ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, tana da kimanin shekaru 16 zuwa 17.

Ta ce tana zaune a Zariya, tana aure kuma Allah Ya albarkace ta da ƴaƴa uku. Ta fara aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika, inda har yanzu take aiki. Ta kuma halarci ƙasashe da dama domin ƙarin ilimi da ƙwarewa.

Kafin wannan nasara, Dakta A’isha ta taɓa zama Shugabar Ƙungiyar Likitoci Mata ta Nijeriya reshen Kaduna, sannan ta riƙe muƙamin Sakatariyar Ƙungiyar Likitocin Jihar Kaduna.

Da aka tambaye ta saƙon da take da shi ga abokan aikinta, ta ce tana godiya bisa amincewar da suka nuna mata, tare da ɗaukar alƙawarin kare haƙƙinsu da yin aiki da gaskiya da adalci. 

Ta kuma yi kira gare su da su haɗa kai domin ci gaban ƙungiyar da inganta harkokin kiwon lafiya.

Game da yadda za ta tabbatar da adalci duk da bambancin addini da ƙabila a cikin ƙungiyar, Dakta A’isha ta ce NMA ƙungiya ce ta ƙwararru masu ilimi da sanin ya kamata, don haka za ta yi shugabanci ba tare da nuna son kai ba.

A ƙarshe, ta yi kira ga duk wanda yake da shawarar ci gaba da ya kawo ta, tana mai gode wa mijinta, iyalanta da duk waɗanda suka ba ta goyon baya wajen cimma wannan nasara. Ta yi addu’ar Allah Ya ɗaukaka Jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.

Mustapha
Idris Umar
+ postsBio
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Yadda Aka Gudanar Da Taron Cikar Sarkin Zazzau Shekaru 6 Akan Karagar Mulki A Zariya
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    ABU Ta Naɗa Kankia Magatakarda, Hussaini A Matsayin “Bursar”
  • Idris Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-umar/
    Sanata Shehu Sani Ya Nemi Gwamnonin Arewa Su Tallafa Wa Bikin Al’adu Na ABU Zariya

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Labarai

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Next Post
Mustapha

Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.