Kamar a yau ne tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya naɗa Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Masarautar Zazzau, a shekarar 2020.
A wani kayataccen bikin ƙaddamar da littafi domin murnar cikar mai martaba, Sarkin Zazzau, Amb. Bamalli shekaru 6 akan mulki a Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yabi Sarkin a yayin da ya kasance babban bako a taron.
Taron ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Arc. Mohammed Namadi Sambo; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar; da kuma Sarakunan Gargajiya masu daraja ta ɗaya da na biyu daga sassa daban-daban a fadin Nijeriya.
Haka kuma, sauran manyan baki, jami’an gwamnati, malamai, jiga-jigan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci taron domin taya Mai Martaba Sarkin Zazzau murnar cika shekaru shida a kan karagar mulkin masarautar.
An gudanar da bikin ne a matsayin wani bangare na tunawa da shekaru shida da Ambasada Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya shafe yana jagorantar Masarautar Zazzau.














