ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ADC Ta Nemi Kotu Ta Hanzarta Yanke Hukunci Kan Rikicin Shugabancin Jam’iyyar

by Muhammad
4 months ago

Jam’iyyar ADC ta rubuta wa Babbar Alƙalin Nijeriya (CJN), inda ta roƙi a hanzarta yanke hukunci kan ƙarar da ke gaban Kotun Ƙoli dangane da rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

A cikin wasiƙar da aka rubuta ranar 28 ga Afrilu, 2026, jam’iyyar ta hannun lauyoyinta ta bayyana buƙatar gaggawa domin kauce wa illa ga shirin ta na shiga zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarar na da alaƙa da takaddamar shugabanci tsakanin ɓangaren David Mark da kuma na Nafiu Bala Gombe tare da wasu.

ADVERTISEMENT

Jam’iyyar ta bayyana cewa Kotun Ƙoli ta riga ta saurari ƙarar a ranar 22 ga Afrilu, inda ta ajiye hukunci, amma har yanzu ba a bayyana ranar yanke hukuncin ba.

A cikin wasiƙar, lauyoyin ADC sun jaddada cewa jinkirin yanke hukunci na iya haifar da mummunar illa ga tsarin jam’iyyar, musamman dangane da sahihancin shugabancinta.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Sun ce hukuncin kotunan da suka gabata ya janyo rashin tantance sahihin shugabancin jam’iyyar, lamarin da ya haifar da ruɗani kan wanda ke da ikon wakiltar ADC a hukumance.

Haka kuma sun bayyana damuwa cewa INEC na iya ɗaukar matakai bisa hukuncin da ake da shi a halin yanzu, wanda ka iya ƙara dagula lamarin idan ba a yanke hukunci cikin gaggawa ba.

Lauyoyin sun gargadi cewa idan aka ci gaba da jinkiri, akwai yiwuwar ADC ta rasa damar shiga zaɓen 2027, saboda cika wa’adin tsarin zaɓe.

Sun ƙara da cewa hakan zai iya tauye haƙƙin miliyoyin ’yan Nijeriya da ke goyon bayan jam’iyyar wajen shiga harkokin siyasa.

Duk da amincewa da cunkoson aiki da ke gaban Kotun Ƙoli, sun roƙi Babbar Alƙali da ta sa baki domin tabbatar da cewa an yanke hukunci cikin gaggawa, suna mai jaddada cewa “jinkirin adalci, tauye adalci ne.”

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Wakilin Sin: Matsalolin Mashigin Hormuz Sun Samo Asali Ne Daga Ayyukan Soji Da Amurka Da Isra’ila Suka Kaddamar Kan Iran

Wakilin Sin: Matsalolin Mashigin Hormuz Sun Samo Asali Ne Daga Ayyukan Soji Da Amurka Da Isra'ila Suka Kaddamar Kan Iran

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.