ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amirul Hajj Na Kano Ya Caccaki NAHCON Kan Halin Da Alhazai Suka Fuskanta A Saudiyya

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Amirul Hajj na jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulƙadir, ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin rashin kulawar da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta yi wa alhazan jihar yayin aikin Hajjin 2026 a ƙasa mai tsarki.

Da yake magana ta bakin mataimakinsa, Sarkin Ƙaraye, Muhammadu Maharaz, Amirul Hajj ya ce alhazan Kano sun fuskanci matsaloli da dama tun daga isowarsu Saudiyya. Ya ce mafi yawan alhazan sun shafe ƙasa da kwana biyu a Madinah maimakon kwanaki hudu ko biyar kamar yadda alhazan wasu jihohi suka samu.

Ya kuma koka kan jinkirin jigilar alhazan Kano zuwa Saudiyya, yana mai cewa hakan ya jefa mutane cikin wahala da damuwa. Haka kuma ya soki ingancin abincin da aka riƙa bai wa alhazai a Madina da Jeddah, yana mai cewa a wasu lokuta ma ba a ba wasu alhazan abinci kwata-kwata ba.

ADVERTISEMENT

Amirul Hajj ya kuma nuna damuwa kan rashin bai wa wasu alhazai katin Nusuk, wanda ya ce ya hana su gudanar da wasu ibadu cikin sauki. Ya bayyana cewa wasu alhazan sun shafe sama da sa’o’i biyar a cikin motocin bas bayan isa Makkah saboda matsalar katin, lamarin da ya fi shafar mata da tsofaffi.

Da yake mayar da martani, Daraktan Horaswa da Bincike na NAHCON, Abubakar Abubakar Yargawal, ya ba da hakuri kan matsalolin da aka fuskanta tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ɗauki matakan gyara domin inganta walwala da jin daɗin alhazan Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

MASU ALAKA

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa
Manyan Labarai

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa
Manyan Labarai

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Next Post
Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

July 16, 2026
M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Tinubu Yana Zuba Kyawawan Ayyuka A Nijeriya – Ganduje

Ganduje Ya Buƙaci A Yi Siyasar Aƙida Domin Inganta Dimokuraɗiyya A Nijeriya

July 16, 2026
Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.