A yau Laraba ne aka bude bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa wato “Canton Fair” karo na 138 a birnin Guangzhou.
A wannan karo, kamfanoni sama da dubu 32 sun halarci bikin, ciki har da kamfanoni masu ci gaba a fannoni da dama sama da dubu 11, adadin da ya zarce na bukukuwan da aka gudanar a baya.
Cikin bikin na wannan karo, an kara yankunan nune-nunen kayayyaki zuwa 179 sakamakon bunkasar harkokin cinikayyar waje, an kuma kafa sabbin yankuna guda 9 domin nuna kayayyakin sanyawa na fasahar AI, da jiragen sama maras matuki dake amfanar da al’umma, da kuma na’urori da kayayyakin da ake kafawa a cikin lambu da dai sauransu.
A yayin biki na wannan karo, za a tura karin sabbin kamfanoni, da sabbin kayayyaki, har ma da sabbin fasahohi zuwa kasashen duniya, domin tallafa wa al’ummomin kasa da kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)














