ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Damƙe Wata Yarinya Da Ta Shirya Garkuwa Da Kanta A Edo

by Rabi'u Ali Indabawa
8 months ago
Edo

Rundunar ƴansandan Jihar Edo ta kama wata yarinya ƴar shekara 18, Obehi Odine, bisa zargin shirya sace kanta da kanta, yayin da aka kuma kama wasu mutum 11 da ake zargin suna da hannu a wata ƙungiyar sace-sace.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, Eno Ikoedem, ya fitar ranar Talata, ya ce an ƙwato kayayyakin shaida da suka haɗa da makamai a yayin gudanar da ayyukan.

Sanarwar ta ce, “An kama wata da ake kira Obehi Odine  ƴar shekara 18, bisa laifin shirya sace kanta tare da neman kuɗin fansa na Naira miliyan 10.

ADVERTISEMENT
  • Matawalle Na Amafani Da Jami’an Tsaro Don Tsorata ‘Yan Adawa – Kakakin Gwamnan Zamfara 
  • ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Daga Cikin Likitoci 2 Da Suka Sace A Edo

Ta amsa laifinta, inda ta tabbatar da cewa ta ƙirƙiri lamarin ne da gangan domin damfaro kuɗi.”

A wani aiki mai nasaba da haka a Ubiaja, rundunar ta ce ta samu wata babbar nasara ta hanyar dabarar binciken daji.

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

“Baturen ƴansanda na sashen Ubiaja (DPO) da kansa ya jagoranci wani haɗaɗɗen aikin binciken daji a yankin Akwocha Camp da dazukan da ke maƙwabtaka, tare da haɗin gwiwar sojojin Nijeriya da Hukumar Tsaron Jihar Edo (ESSC).

“An kai samame wani wurin ɓoye a cikin daji, wanda rundunar jiragen drone ta gano ta hanyar bayanan sirri daga sa ido ta sama, a matsayin wurin da ake zargin ana amfani da shi wajen sace mutum da ajiyar kayan aiki.”

“Hakan ya kai ga kama mutum 11 maza da ake zargin mambobin wata shiryar ƙungiyar garkuwa da mutum ce mai tsari.

Kayan shaida da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin gargajiya guda 24, adda (cutlass) guda 17, gatari na yaƙi guda uku, foda bindiga, fitilun hannu, wayoyin salula, kayan aikin fitila mai amfani da hasken rana, tsafe-tsafe iri-iri, babur guda ɗaya, da kuɗi Naira 209,700, da sauran kayayyaki.”

A halin da ake ciki, Kwamishinan Ƴansanda na jihar, Monday Agbonika, ya gargaɗi jama’a da su guji bayar da rahoton sace-sacen ƙarya ko shiga wasu ayyukan yaudara.

Ya ce irin waɗannan ayyuka na ɓata muhimman kayan aikin tsaro, suna karkatar da hankali daga ainihin gaggawa, suna haifar da firgici ba tare da dalili ba, tare da raunana amincewar jama’a. “Duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a gaban doka,” in ji shi.

Agbonika ya sake jaddada aniyar rundunar ta ci gaba da aikin tsaro ta amfani da fasaha, tsauraran matakan mamaye dazuka, da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri domin tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka a faɗin jihar.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ƴansanda haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci.

Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutum ne sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 100 domin sakin ƴan Imoga takwas da aka sace a daren Juma’a.

Sarkin Imoga Kingdom, Okpahi na Imoga, Oba Patrick Obajoye, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho.

Ya ce an sace mutumn ne a Star Boy Hotel da ke kan hanyar Imoga–Ibillo a Edo ta Arewa.

Oba Obajoye ya bayyana cewa mutumn sun je Ibillo ne domin wani biki, sannan suka yanke shawarar kwana a Star Boy Hotel, wanda shima mallakin wani ɗan Imoga ne.

Ya ƙara da cewa masu garkuwa da mutumn sun zo otal ɗin sanye da kayan sojoji, suna ɗauke da abin sha, suka yi kamar suna jiran wani ne.

Edo
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Labarai

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Next Post
An Kammala Gwaji Na Farko Na Shirye-shiryen Murnar Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na Shekarar 2026

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.