ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago

Wasu alƙaluman hukumar Lafiya ta duniya WHO sun bayyana cewa mutum fiye da dubu 1,300 ne tsananin zafi ya kashe a ƙasashen Turai daga ranar 21 ga watan da muke na Yuni kawo yanzu, wanda ke matsayin adadi mafi yawa da nahiyar ta taɓa gani a tarihi.

Tsananin zafin da ke matsayin mafi ƙololuwa da nahiyar ta Turai ta taɓa gani, a Faransa kaɗai mahukuntan ƙasar sun ce kusan mutum 1000 tsananin zafin ya kashe daga Larabar da ta gabata zuwa yammacin Lahadi yayin da rahoton WHO ke cewa a jumlace akwai mutanen da yawansu ya haura dubu 1,300 waɗanda zafin ya kashe tun bayan tsanantarsa a ranbar 21 ga watan da muke.

Ko a ƙarshen mako an ga yadda tsananin zafin ya ci gaba da tsananta koda yake ya fara nausawa yankin gabashin nahiyar wato ƙasashen da bisa al’ada aka san su da yanayi na tsananin sanyi kuma tuni wasu daga cikin ƙasashen suka fara fitar da bayanan ƙaruwar masu mutuwa da waɗanda ke kamuwa da cutuka sanadiyyar zafin.

ADVERTISEMENT

Miliyoyin turawa ne suka tare a wuraren shaƙatawar bakin ruwa cikin kwanakin ƙarshen mako don samun sassauci daga matsanancin zafi a wani yanayi da masana a ɓangaren lafiya ke ci gaba da gargaɗin mahukuntan don ɗaukar matakan bai wa jama’a kariya.

A ranar Lahadi kaɗai Turawa miliyan 191 sun fuskanci zafin da ya kai maki 35 a ma’aunin Celcius yayin da aka ga zafi na daban wanda ya kai ƙololuwa a ƙasashen Jamus da jamhuriyyar Czech kana Hungary da kuma Poland da zafinsu ya kai maki 41 karon farko da nahiyar ke ganin irin haka.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

Hasashen masanan yanayi daga Jamus ya nuna cewa al’ummar nahiyar miliyan 381 banda Turkiyya za su ga tsananin zafin da zai riƙa haura maki 30 lamarin da Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ke cewa wajibi ne hukumomi su samar da matakan sassauci ga jama’a don kaucewa ƙaruwar mace-mace da rashin lafiya mai alaƙa da zafin.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Messi Da Mbappé Na Jagorantar Cin Ƙwallaye A Gasar Kofin Duniya

Messi Da Mbappé Na Jagorantar Cin Ƙwallaye A Gasar Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.