An gurfanar da wasu makiyaya biyu, Shehu Umaru mai shekaru 40 da Muhammadu Riskua mai shekaru 30, a gaban wata Kotun Majistare a Ado-Ekiti bisa zargin kiwo ba bisa ƙa’ida ba.
Mai gabatar da ƙara, ASP Akinwale Oriyomi, ya shaida wa kotun cewa mutanen sun yi kiwon shanu a wata gonar da ba a ba da izinin kiwo ba a dajin Itapaji-Ekiti ranar 11 ga watan Agusta.
Ya ce abin da ake zargin mutanen da aikatawa ya saɓa wa dokar Jihar Ekiti da ta haramta kiwon shanu da sauran dabbobi masu cin ciyawa a wasu wurare.
Mutanen biyu sun musanta zargin.
Lauyansu, Gboyega Abiola, ya buƙaci kotun ta bayar da su beli.
Alƙalin Majistaren, Abayomi Adeosun, ya bayar da belinsu kan Naira 50,000 kowanne, tare da mutum ɗaya da zai tsaya musu.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Satumba.














