Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta tura jami’ai 250 da suka kammala ɗaukar horon yaƙi da sarrafa makamai zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyakar jihar domin inganta tsaro.
Jami’an sun kammala ɗaukar horon na tsawon wata guda kan dabarun yaƙi da sarrafa makamai kafin bikin kammala horon da aka gudanar a filin fareti na rundunar ’yansandan Mobile Force ta 9 (PMF) da ke Hotoro, Kano.
A cewar Kakakin Rundunar ’yansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, an gudanar da horon a rundunar PMF ta 9 da ke Hotoro da kuma PMF ta 52 da ke Challawa.
An horar da jami’an kan sarrafa makamai, harbi, dabarun yaƙi da sauran hanyoyin gudanar da ayyukan tsaro.
Haka kuma, sun samu horo kan kare haƙƙin bil’adama, amfani da ƙarfi da makamai, aikin leƙen asiri da yaƙi da ayyukan ta’addanci.
Kwamishinan ’yansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tura jami’an zuwa yankunan da ke kan iyakokin jihar na da nufin ƙarfafa tsaro da kuma tabbatar da gaggawar kai ɗauki ga al’umma idan aka samu matsalar tsaro.
“Jami’ai 250 da suka kammala horon a yau za a tura su ƙananan hukumomin da ke kan iyakar Jihar Kano,” in ji Bakori.
Ya umurci jami’an da su kasance cikin shiri a kowane lokaci, su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa tare da mutunta haƙƙin jama’ar da ke bin doka.
Kwamishinan ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da shirya horon ƙara wa jami’ai ƙwarewa domin inganta ayyukansu da kuma tsaron kansu.
Ya gode wa gwamnatin Jihar Kano da al’ummar jihar bisa ci gaba da bai wa rundunar goyon baya, sannan ya umarci jami’an da su koma wuraren da aka tura su domin fara aiki.














