Aƙalla mutane 11 ake fargabar an kashe bayan wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hari ƙauyen Zaranga da ke Karamar Hukumar Gombi a Jihar Adamawa a safiyar Litinin.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shiga ƙauyen da sassafe, inda suka riƙa harbin mazauna tare da kona gidaje. Ya ce zuwa lokacin da yake magana, an gano gawarwaki 11, yayin da wasu mutane da dama suka bace.
Wani mazaunin ƙauyen ya tabbatar da cewa matarsa da wasu ’yan uwansa biyu na cikin mutanen da aka kashe. A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da laluben dajin domin gano mutanen da aka rasa.
Har zuwa lokacin haɗa rahoton jaridar Vanguard, rundunar ’yansandan Jihar Adamawa ba ta tabbatar da adadin waɗanda aka kashe ba, haka kuma Kakakin Rundunar, SP Suleiman Nguroje, bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.
Saboda haka, ba a iya tantance adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su ba, yayin da bayanan harin da kuma makomar mutanen da aka ce sun bace ke ci gaba da kasancewa ba a fayyace su ba.














