ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

APC A Zamfara Ta Ayyana Cikakken Goyon Bayanta Ga Tinubu Da Dauda Lawal A Zaɓen 2027

by Sulaiman
5 months ago
Zamfara

Jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a babban zaɓen shekarar 2027.

An bayyana wannan matsaya ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2026.

Taron ya haɗa manyan jiga-jigan APC daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da tsofaffin gwamnoni huɗu, zababbun jami’ai, dattawa, wakilan matasa da mata, da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa lokacin gudanar da irin wannan zama ya dace matuƙa, ganin yadda harkokin siyasa ke ƙara ƙarfi yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya jaddada cewa sauya sheƙar da ya yi zuwa APC ba kawai siyasa ba ce, illa wata dabara ce ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin inganta ci gaban Zamfara.A cewarsa, shirin ceto na “Rescue Mission” da gwamnatinsa ke aiwatarwa na wakiltar muradin al’ummar jihar gaba ɗaya, ba na wata ƙungiya ko ɓangare kaɗai ba. Ya ƙara da cewa gwamnati na mai da hankali wajen dawo da zaman lafiya, gina cibiyoyi, da samar da ayyukan ci gaba da za su amfanar da jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Gwamnan ya kuma yi kira ga jiga-jigan jam’iyyar da su gudanar da harkokinsu cikin natsuwa da hikima, yana mai jaddada cewa siyasa na buƙatar sulhu, fahimtar juna da kuma yin aiki tare domin cimma manufa.

Ya yi alƙawarin cewa adalci, gaskiya da bin ƙa’ida za su ci gaba da zama ginshiƙai a dukkan matakan tafiyar da jam’iyyar da gwamnati.

A nasu ɓangaren, tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da Ahmed Sani Yarima, Mahmud Aliyu Shinkafi, Abdulaziz Yari da kuma Bello Mohammed Matawalle sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga jam’iyyar APC tare da marawa Tinubu da Lawal baya domin sake tsayawa takara a 2027.

Sanarwar taron da Ƙaramin Ministan Tsaro na Ƙasa, Matawalle, ya karanta ta bayyana cewa taron ya ba da dama wajen tattauna muhimman batutuwa da suka shafi haɗin kan jam’iyya, daidaita tafiyar gwamnati, matsalolin tsaro, da kuma shirye-shiryen tunkarar manyan zaɓukan gaba.Taron ya kuma ƙarfafa buƙatar ci gaba da haɗin kai a tsakanin mambobin APC domin tabbatar da nasara a zaɓen 2027, tare da jaddada muhimmancin bin tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida da kuma kauce wa duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Harbe-harbe: Trump Da Mataimakinsa Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Babban Taron ‘Yan Jarida

Harbe-harbe: Trump Da Mataimakinsa Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Babban Taron 'Yan Jarida

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.